Wasu ‘Yan bindiga sun sace Malamin Makaranta da Fastoci 2 a Kogi

Wasu ‘Yan bindiga sun sace Malamin Makaranta da Fastoci 2 a Kogi

Ba da dadewa ba mu ka ji labari cewa wasu ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu Malaman addini a tsakiyar Najeriya. Wannan mummunan abu ya faru ne a wani Kauye da ke cikin Jihar Kogi.

Daily Trust ta rahoto cewa wasu ‘Yan bindiga sun sace wasu Malaman Addini da kuma wani Malamin Makaranta a Garin Irepeni da ke cikin Karamar Hukumar Adayi da ke kan hanyar zuwa Garin Okene a cikin Jihar Kogi sun yi garkuwa da su.

Wasu ‘Yan bindiga sun sace Malamin Makaranta da Fastoci 2 a Kogi
An sace wasu Bayin Allah a hanyar Okene zuwa Kabba

Malamin addinin da aka sace shi ne Rabaren Leo Micahel wanda babban Limamin Darikar Katolika ne na addinin Kirista a wani coci da ke Garin Obajana. Labarin da mu ke ji shi ne har yanzu dai an rasa gane dayan Faston da aka yi gaba da shi.

Bayan nan kuma an sace wani babban Malamin Makaranta mai suna Aronimu Babatunde Samuel. Aronimu Samuel yana koyarwa ne a wata kwalejin ilmi da ke Garin Kabba. Malamin ya shiga hannun ‘Yan bindigan ne a hanyar Okene zuwa Kabba.

KU KARANTA: Buhari ya daure kan sa da kan sa a game da batun Kemi Adeosun

Bishof Peter Adinoyi ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa daga wani daji ne ‘Yan bindigan su ka fito su ka sace Manyan Malaman. Dayan Faston dai babba ne a cocin RCCG. Yanzu dai ‘Yan bindigan su nemi a biya Miliyan 14 kafin su saki wadannan Malamai.

Kafin nan ma dai an nemi a biya kudi har Naira Miliyan 50 ne kafin su saki wadannan Fastoci da ake ji da su. Jami’an tsaro dai sun ce ba su da labarin faruwar wannan abu ko da aka tuntube su. Garkuwa da mutane dai na nema yayi kamari a Kasar a yanzu.

A Ranar Lahadi kun ji cewa Masu garkuwa da mutane sun yi ta’asa a hanyar Abuja zuwa Kaduna inda aka kashe wani babban Soja da ‘Dan Sanda da wata babbar Farfesa daga Jihar Katsina bayan an sace mutane da dama a hanyar zuwa Birnin Tarayyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng