Sanata ya tona asirin makircin da Saraki da Dogara ke kullawa Buhari
Sanata Abu Ibrahim mai wakiltan yankin Kudancin Katsina ya yi kira ga shugabanin jam'iyyar APC su kori shugabanin majalisar tarayya, Bukola Saraki da Yakubu Dogara saboda yana ingatanciyyar hujjar cewa shugabanin jam'iyyar sun shirya tsige shugaba Muhammadu Buhari.
A yayin da yake hira da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, Sanata Ibrahim idan a kayi la'akari da abubuwan dake faruwa a majalisar, za'a fahimci cewa Saraki da Dogara suna da wata manufa kuma hakan yasa jam'iyyar APC bai dace ta amince dasu ba.
Sanata Ibrahim wanda shine shugaban kungiyar magoya bayan Buhari yace tun a baya dama ya yi hasashen cewa wasu 'yan majalisar zasu fice daga jam'iyyar APC saboda haka ficewarsu bai bashi mamaki ba.
DUBA WANNAN: Dan takarar gwamna a PDP ya yi korafin cigaba da tsare shi ga IG
Dan majalisar yace ficewar Sanata Abdullahi Danbaba na jihar Sokoto ne kawai ya bashi mamaki, "Na san wadanda suke daukan Saraki a matsayin abin bautarsu, saboda duk inda Saraki ya nufa, zasu bi shi. Sai dai kuskuren da su kayi shine sun manta cewa tushen siyasa shine kusanci ga talakawa.
"Babu wanda zai ce Saraki ne ya yi sanadin nasarar Isa Misau da Suleiman Nazif na jihar Bauchi, an zabe su ne saboda albarkacin Buhari kuma zasu rasa kujerunsu. Saraki ba zai iya cetonsu ba. Ba ma su iya ziyaratar mazabunsu.
Sanata Ibrahim ya yi kira ga Saraki da Dogara suyi murabus daga jam'iyyar APC domin a cewarsa su ba mambobin APC bane. "Abinda yasa basu koma PDP ba shine basu son rasa kujerunsu. Amma zamu tabbatar sun fice daga APC. Idan da za'a bi shawara ta da an kore su daga APC. Zamu samu zaman lafiya idan sun fice.
Sanata Ibrahim yace ficewar Saraki da Dogara ba zai hana shugaba Muhammadu Buhari samun nasara a babban zaben 2015 ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng