Allah mai iko: Bayan shekara 7 da aure, wata mata ta haifi 'yan 5 a Arewa

Allah mai iko: Bayan shekara 7 da aure, wata mata ta haifi 'yan 5 a Arewa

Wasu ma'aurata cike da farin ciki da annashuwa kamar yadda muka samu daga majiyar mu a BBC Hausa, sun samu karuwa bayan da matar ta haifi jarirai biyar ringis a wani asibitin da ke a garin Jos na babban birnin jihar Filato dake a yankin Arewacin Najeriya.

Kamar yadda muka samu dai, a farkon satin nan ne dai matar mai suna Hajiya Jamila tare da mijin na ta Alhaji Garba suka samu karuwar bayan shafe shekaru bakwai da aure ba tare da haihuwa ba.

Allah mai iko: Bayan shekara 7 da aure, wata mata ta haifi 'yan 5 a Arewa

Allah mai iko: Bayan shekara 7 da aure, wata mata ta haifi 'yan 5 a Arewa

KU KARANTA: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharuddan zaman lafiya a PDP

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jariran biyar da ta haifa sun hada da maza uku, da kuma mata biyu sai dai kuma jim kadan bayan haihuwar, dukka mazan suka rasu.

A wani labarin kuma, Shugaban masana sararin samaniya da kuma hasashen yanayi a jami'ar tarayyar Najeriya dake a garin Nsukka, Farfesa Augustine Ubachuku yayi hasashen cewa a gobe Juma'a wata zai yi masassarar da bai taba yi ba mai tsawon gaske.

Farfesa Ubachuku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da manema labarai a dakin taron jami'ar da safiyar yau, inda kuma ya shawarci al'umma da su kwantar da hankalin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel