Dalilai biyar da zaku so ji don saduwa lokacin iyali na da ciki
- Kiwon Lafiya ga mai ciki baya nufin tayi darban a gida
- Ana son a sadu da mai ciki domin lafiyarta
- Ba'a son wuce gona kuma da iri ga masu zumudi
A lokutan da iyali suka dauki ciki, akan dauka shike nan soyayya ta qare sai tsir da yau, laulayi da kara qiba, amma a likitanci abiin ba haka bane, don kuwa ana son ma'aurata su qara dankon soyayya a wannan lokaci.
An kasa zaman daukar ciki kashi uku, wata uku-uku, na farko da na biyu da na karshe.
Ba'a son a yawaita saduwa a watannin farko don kar dan tayin ya tsiyaye, a wannan lokaci so ake a lallaba a kai zangon gaba.
DUBA WANNAN: Zata mayar da sadaki don a raba auren shekaru 8
A na biyu, ana son a dinga saduwa sosai don wadannan dalilai:
1. Motsa jiki ne saduwa, ba'a son a bar mai ciki ta kara qiba, ko jininta ya hau.
2. Ana son maniyyi ya dinga zagaya mahaifa don yanada sinadarai masu gyara jiki.
3. Saduwar kan qara danqon soyayya a wannan lokaci tsakanin ma'aurata.
4. A lokutan saduwa, jiki kan saba da murda-murda, wadda kan bada kwarin gwiwar haihuwa cikin sauki.
5. Saduwa kan sanya jiki rage jin radadin sauyin jiki, da ma lokutan haihuwa, kuma yakan rage laulayi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng