Likita da aka gano ashe mai gadi ne yake wa mutane allura

Likita da aka gano ashe mai gadi ne yake wa mutane allura

Wani mai gadi, Salisu Usman, ya amsa laifin yiwa likitoci sojan gona a yayin da aka gurfanar dashi gaban Alkalin kotun majistare dake Legas inda ya fadawa kotu cewa ya dade yana yaudarar mutane da cewa shi likita ne.

Alkalin kotun, Mrs. B.O. Osunsanmi, ta bayar da umurnin a cigaba da tsare Usman a gidan yari na Kirikiri har zuwa ranar 20 ga watan Yuli saboda a bawa kotu damar nazarin hujojin da aka gabatar a kansa da hukuncin da za'a yanke masa.

Usman mai shekaru 28 dake zaune a Oluwalogbo, Ifesun dake Ayobo kusa da Legas ya roki kotu tayi masa rangwamae bayan ya amsa cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Dubun Malam Salisu maigadin asibiti dake duba marasa lafiya a asibiti har ya yi masu allura ta cika
Dubun Malam Salisu maigadin asibiti dake duba marasa lafiya a asibiti har ya yi masu allura ta cika

A cewar dan sanda mai shigar da kara, ASP. Ezekiel Ayorinde, Usman ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Yuli a Baden Junction dake Ayobo.

DUBA WANNAN: Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Yace an damke Usman dauke da wata jaka kuma cikin jakar akwai kayayakin aikin likita, kwayoyi da kuma kayayakin tiyata.

"Wanda ake tuhumar dake ikirarin shi Likita ne ya kasance yana duba marasa lafiya, yana bayar da magani, ya kan kuma siyar da magungunan masu hatsari wanda ba'a sayar dasu sai da izinin kwararen Likita.

"An samu magunguna daban-daban cikin jakar tare da Sirinji da allura da wasu kayayakin aikin likita.

"Sai dai lokacin da aka bukaci ya bayyana katin shedan cewa shi Likita ne, sai ya fara kame-kame.

"Daga nan ne ya bayyana cewa shi ba Likitan gaskiya bane kuma aka tisa keyarsa zuwa caji ofisi," inji mai shigar da karar.

Ayorinde yace wannan laifin ya sabawa sashi 251(e)(f) da dokar masu laifi na jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa sashin dokar ta tanadar da hukuncin zaman gidan kurkuku na shekaru biyu ga masu irin wannan laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: