Jam'iyyar APC zata kai jam'iyyar R-APC kotu

Jam'iyyar APC zata kai jam'iyyar R-APC kotu

A jiya Litinin ne Jam'iyar APC tace zata kai shugabanni da kuma mambobin sambuwar jam'iyyar Reform All Progressive Congress (R-APC)

Jam'iyyar APC zata kai jam'iyyar R-APC kotu
Jam'iyyar APC zata kai jam'iyyar R-APC kotu

A jiya Litinin ne Jam'iyar APC tace zata kai shugabanni da kuma mambobin sambuwar jam'iyyar Reform All Progressive Congress (R-APC).

Mai bawa jam'iyar shawara akan doka Mr Babatunde Ogala ne ya sanar da hakan a Abuja a yayin bayyana ra'ayin sa akan samar da kungiyar wanda wani jigo na jam'iyar ta APC Alhaji Buba Galadima ya tsara.

DUBA WANNAN: Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

Ogala ya bayyana jawabin Galadima akan ra'ayin sa dangane da R-APC da dawo da hannun agogo baya bayan dumbin nasarori da aka samu dangane da juyin mulki wanda Yan Nageriya suka sha fama kafin zuwan dimokradiyya.

Yace wasu daga cikin wadanda suka raba jam'iyar sun bazama sun shiga gari domin inganta gudanarwar su.

Sabuwar jam'iyar ta R-APC wadda ta tashi daga APC a ranar Laraba an kafa mata kwamitoci na kasa dana jaha wadanda ke kananan hukumomi 774 dake fadin kasar nan.

Yace "Saboda muna gwada jam'iyun siyasa da dama APC bazata hana Galadima samar da tashi jam'iyar ba idan har yana kwadayin hakan," amma kuma jam'iyar bazata bari Galadima yayi amfani da alamar taba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng