Najeriya tana cikin jerin Kasashen da su ka hadarin zama ga mata
Mun samu labari cewa wani bincike da aka yi a Kasar waje ya nuna cewa akwai Kasar Najeriya cikin jerin Kasashen da su ke da hadarin zama matuka ga mata a duk fadin Duniya. Thomson Reuter’s ne yayi wannan bincike.
Najeriya dai ta samu shiga cikin sahun farko na kasashen da ke da hadarin zama ga mata a shekarar nan ta 2018 da ake ciki. Kasar da ta zo kan gaba a wannan jeri dai ita ce Indiya inda ake samun yawan fyade na ‘Ya ‘ya mata.
Bayan Kasar Indiya sai irin su Siriya da Somaliya da Fakistan da ma Afghanistan. A wadannan kasashen dai Musulmai su ne akasari. A cikin kasashen da aka jero dai har da Kasar Saudi Arabia inda yanzu mata ke samun sakewa.
KU KARANTA: Wasu mutane 10 sun mutu a hanyar Kano ta hadarin mota
Kasar Amurka da ice ta zo ta 10 a binciken da aka gudunar. Amurka ce Kasar da ba ta cikin Nahiyar Asiya da kuma Afrika da ta shiga cikin jerin.
Kasashen dai su ne:
1. Indiya
2. Afghanistan
3. Siriya
4. Somaliya
5. Saudi Arabia
6. Fakistan
7. Kongo
8. Yemen
9. Najeriya
10. Amurka
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng