Tsokalo tsuliyar Dodo: Yan bindiga sun hallaka Dakarun Sojoji guda 2
Wasu gungun yan bindiga dadi sun kashe dakarun rundunar Sojin kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da yan bindigar suka kai musu a cikin karamar hukumar Guma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun shirya wani tarko ne a daidai lokacin da Sojojin ke sintiri a a tsakanin kauyukan Umenger da Bakin korta, duk a cikin mazabar Mbadewem, a inda Sojoji biyu suka mutu, wasu kuma suka jikkata.
KU KARANTA: Manyan dillalan wiwi guda 88 sun fada komar jami’an hukumar NDLEA
Wasu mazauna kauyen sun bayyana cewa yan bindigan sun yanke gadojin dake kaiwa zuwa kauyukan Nassarawa da na jihar Benuwe domin su hana ma Sojoji damar bin sawunsu, dayake ajali yayi kira, sai Sojoji suka doshi wajen bayan sun gano shirin yan bindigar.
Isarsu ke da wuya sai suka tarar da yan bindiga makil cike da wani sansani da suka bude, anan aka fara barin wuta, ana musayar yawu. Shima shugaban karamar hukumar Guma, Anthony Shawon, ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana cewa akwai sama da yan bindiga 3,000 a wani sansani dake cikin dazukan jihar Nassarawa, inda daga nan ne sua kai hari cikin karamar hukumar Guma.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin Arewa ta tsakiya, Alhaji Danladi Ciroma ya bayyana ma majiyarmu cewar bashi da masaniya game da lamarin, “An riga an fatattaki yan bindigan dake wajen, mai sake mayar dasu wajen, amma dai gaskiya ban sani ba.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng