Ni ba mahaukaci bane PDP na son amfani da ni da kudina wajen farfado da jam’iyyar sannan su marawa Makarfi baya - Atiku

Ni ba mahaukaci bane PDP na son amfani da ni da kudina wajen farfado da jam’iyyar sannan su marawa Makarfi baya - Atiku

A daidai lokacin da guguwar iskar zaben 2019 ke dada kadowa, yan siyasa na cigaba da gyara kwanjinsu don ganin sun haye kujerun da suke nema.

Haka zalika jam’iyyu na kokarin ganin kwarzon da zasu tsayar domin kwashe kujerar shugabancin kasa daga hannun APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai labarin dake zuwa mana sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar y bayyana cewa ya harbo jirgin jam’iyyarsa ta PDP.

A cewarsa shi ba mahaukaci bane domin ya san cewa jam’iyyar na son yin amfani dashi da kudinsa wajen farfado da kanta sannan daga baya sais u marawa Ahmad Makarfi baya.

Ni ba mahaukaci bane PDP na son amfani da ni da kudina wajen farfado da jam’iyyar sannan su marawa Makarfi baya - Atiku
Ni ba mahaukaci bane PDP na son amfani da ni da kudina wajen farfado da jam’iyyar sannan su marawa Makarfi baya - Atiku

Rariya ta ruwaito inda Atiku yace: “Suna So Su Yi Amfani Da Ni Da Kuma Kudina Wajen Farfado Da Jam'iyyar PDP Sannan Daga Baya Su Marawa Ahmad Makarfi Baya A Matsayin Dan Takaran Shugaban Kasa A Karkashin PDP, Ni Ba Mahaukaci Bane”.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

Idan baza ku manta ba daga cikin masu hararar kujerar shugaban kasa a PDP akwai Atiku Abubakar, Sule Lamido , Ahmad Makarfi da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng