Hariji ne baya barina na huta kwata-kwata - Cewar matar da ta nemi a raba aurenta da mijinta

Hariji ne baya barina na huta kwata-kwata - Cewar matar da ta nemi a raba aurenta da mijinta

- Wani mutum mai shekaru 72 mai suna Funsho Amos ya amince da bukatar matarshi ta tsinke igiyar aurensu

- Ayo Amos mai shekaru 40, 'yar kasuwa ce da ta maka mijinta a kotu don a rabasu saboda baya kwanciyar aure da ita na shekaru uku

- Ta bayyana cewa, tana bukatar a tsinke igiyar aurensu ko zata samu rabon haihuwa a nan gaba

Funsho mai shekaru 72 a duniya ya yi murabus daga aiki babu dadewa kuma kotu ta tsinke igiyar aurenshi da matarshi. An zargeshi da rashin kwanciya da matar ne na shekaru uku.

Wata kotu dake Legas, a ranar Talata ta amince da bukatar Mrs Ayo Amos, wacce ta bukaci kotun da ta tsinke igiyar aurenta da Funsho a dalilin rashin kwanciyar aure da ita na shekaru uku.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, yayin yanke hukuncin, yace ta bayyana ma'auratan sun gaji da zama da juna kuma duk yunkurin sassanci ya gagara.

"Tunda dukkan ma'auratan sun amince da tsinke igiyar aurensu, wannan kotu bata da wani zabi da ya wuce ya kashe auren.

"A don haka ne kotun ta tsinke igiyar auren da ke tsakanin Mrs Ayo Amos da Funsho Amos a yau. Daga yau dukkanku kun daina amsa sunan mata da miji. Kowannenku zai iya tafiya ba tare da hantara ko tsangwama ba. Kotu tana muku fatan alheri a rayuwa," Koledoye ya yanke.

An gano cewa, Ayo 'yar kasuwa ce mai shekaru 40. Ta tunkari kotun ne da bukatar tsinke igiyar aurensu saboda rashin biya mata bukata da mijinta ke yi.

"Mijina baya kwanciyar aure dani na shekaru uku kuma babu dalili. Ya san ina bukatar haihuwa," Ayo ta ce.

KU KARANTA: Tsohon Najadu: Uba ya dirkawa 'yarshi cikin shege har sau biyu ya tsere ya barta da wahala

"Ya bukaci da in kwashe kayana in bar gidanshi saboda bana haihuwa. Ya ce in samu wani namijin, shi bashi da ra'ayina. Ya ki biyan kudin hayar gidanmu da shagonmu kuma ya bukaci mai gidan da ya koreni.

"Na rokeshi kuma 'yan uwana sun rokeshi. Ya sanar dasu cewa baya ra'ayina ne," Ayo ta ce.

"Na bukaci saki amma ya ki bani. Yace babu namijin da zai aureni tunda har ya kwanta dani. Don haka babu bukatar saki a tsakaninmu," ta ce.

Ayo ta yi kira ga kotun da ta tsinke igiyar aurensu don ta samu rabonta a nan gaba.

Funsho yace: "Bana sonta ko kadan yanzu. Ina rokon kotu da ta amince da bukatarta. A tsinke igiyar aurenmu. Ina da 'ya'ya shida, wasunsu na kasar waje. Bana bukatar haihuwa tare da ita," Funsho ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel