Aiki na kyau: Uwargidar Babagana Monguno ta tallafa ma marayu da zawarawa 10,000

Aiki na kyau: Uwargidar Babagana Monguno ta tallafa ma marayu da zawarawa 10,000

Uwargidar hadimin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, Hajiya Nafisa Monguno ta tallafa ma mata zawarawa da yara marayu su dubu goma a jihar Kaduna, inda ta basu kayan abinci da kayan sawa da ma sauran amfani, duk a cikin watan Ramadan.

Rahoton Daily Trust ta bayyana cewar Hajiya Nafisa ta cimma wannan gagarumin nasara ne ta hadin gwiwa tsakanin gidauniyarta, Precious Little Lives Initiative (PreLLi) da gidauniyar Ummulkhairi, da kuma gidauniyar sakandarin kasar Turkiyya, NTIC.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Za’a fara kidayan adadin mutanen da jami’an Yansanda ke ci zarafinsu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cewar Hajiya Nafisa, sun yi haka ne da nufin tallaka ma gajiyayyu a jihar Kaduna, tare da rage musu radadin talauci musamman a watan Ramadan, inda ta kara da cewa ya kamata mutane su taimaka ma gajiyayyu, ba lallai sai masuz arziki ba.

Aiki na kyau: Uwargidar Babagana Monguno ta tallafa ma marayu da zawarawa 10,000
Nafisa

“A matsayina na Musulma, ba sai an fada min na bada taimako saboda Allah ba, saboda Allah ya riga ya umarce mu da yin haka, ta hanyar taimako ne zamu iya magance matsalar shaye shaye daga al’ummarmu dana Almajiranci.

“Idan aka lura dukkaninmu muna da tawaya ta wani fanni, me yiwuwa ne ta bangaren kudi, hankali, ko kuma lafiyan jiki, amma dukkanmu mun taru anan wajen, muna fata Allah ya karbi ibadunmu, kuma ya jikanmu.” Inji ta.

Daga karshe ta yi kira ga marayu da matan da mazajensu suka mutu da su rungumi kaddara kuma su yi hakuri, sa’annan su cigaba da kai kukansu ga Allah, zai share musu hawayensu. Sa’annan ta yaba da kokarin da sauran kungiyoyi suka yi wajen tallafa ma rayon, ta yi kira garesu da kada su gaza.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

o

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel