Annafsu binnafsu: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanya mai matsanancin wahalka ga wani mutumi da ya kashe yarinya a Bauchi

Annafsu binnafsu: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanya mai matsanancin wahalka ga wani mutumi da ya kashe yarinya a Bauchi

Babban Kotun jihar Bauchi ta yanke hukuncin kisa akan wani mutumi, Jaridu Ahmad mai shekaru 33 ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin yi ma wata karamar yarinya Hajara Adamu kisan gilla tare da birne gawarta, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jaridu ya tafka wannan laifi ne a ranar 30 ga watan Agusta na shekarar 2015, da wannan ne Alkalin Kotun, Mai sharia Gurama Muhammad Mahmud ya yanke masa hukuncin kisa, kamar yadda sashi na 221 sakin layi 38 na kundin hukunta manyan laifuka ta tanadar.

KU KARANTA: Makashin maza, maka ke kashe shi: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a jihar Zamfara

Da yake yanke hukuncin, Alkali Gurama yace: “Bayan sauraran dukkanin bayanai, da kuma amsa laifinka da ka yi da kanka, na kama ka Jaridu Ahmad da laifin yi ma Hajara Adamu kisan gilla, don haka ya zama wajibi a kasheka ta hanyar rataye wuyanka har sai an tabbatar ka mutu.”

Annafsu binnafsu: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanya mai matsanancin wahalka ga wani mutumi da ya kashe yarinya a Bauchi
Kotun

A wani labarin kuma wasu masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da wasu jami’an Yansanda guda biyu a garin Fatakwal na jihar Ribas sun yanke ma rundunar Yansandan Najeriya nara miliyan Talatin a matsayin kudin fansar da suke bukata.

Jaridar Punch ta ruwaito Yansandan da aka sata sun hada da Sajan Haladu Muhammad da wani abokin aikinsa da ba’a bayyana sunansa ba, an sace su ne a ranar Laraba, 9 ga watan Mayu a masaukin da suka sauka, yayin da suka je yin wani aiki na musamman a garin Fatakwal.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel