Za a jefa saurayin da ke karya da sunan Sarki Sanusi II a gidan maza

Za a jefa saurayin da ke karya da sunan Sarki Sanusi II a gidan maza

- An jefa wani saurayi da yake damfarar jama’a da sunan Sarkin Kano a kurkuku

- Wannan matashi ya karbi sama da Miliyan 1.85 daga hannun Bayin Allah a baya

- Ana karar wannan yaro da laifin yi wa Sarki karya da ci masa mutunci da damfara

Labari ya zo mana dazu cewa za a jefa wani saurayi mai suna Sultan Bello mai shekara 20 a Duniya da ke amfani da sunan Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a gidan maza a Yau Laraba. Wannan matashi na karbar kudi ne daga jama’a ya jefa a asusun sa.

Za a jefa saurayin da ke karya da sunan Sarki Sanusi II a gidan maza
Za a daure yaron da ke yaudarar Jama’a da sunan Sarkin Kano

Alkalin Kotun Majistare ta Unguwar Jao’ji a Jihar Kano Hassan Ahmad ya nemi a garkame wannan Matashi da ke Sojan gona da sunan Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II a kafafen sadarwa na zamani inda ya daga karar zuwa nan gaba kadan.

KU KARANTA: Ba a dawo da wasu 'Yan makarantar Dapchi gida ba

A cikin Watan Fubrairu dama ‘Yan Sanda su ka shiga da wannan yaro Kotu bayan da aka zarge shi da yaudarar jama’a da dama a kafafen zamani na Instagram. Ana zargin wannan Matashi da damfarar wasu mutane makudan kudi da sunan Mai martaba.

Wannan yaro da ake kara tuni ya fadawa Kotu cewa tabbas ya aikata laifin da Lauya Haziel Ledapwa ke karar sa da su. Sultan ya karbi kudi kusan Miliyan 2 daga hannun Baraka Sani, Sadiq Saflan, Sadiq Sani, Aisha Ahmad, Surajo Zakari da wasu ma dai a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng