An bawa direbobin tanka sa’o’i 48 su bar saman gadojin Legas

An bawa direbobin tanka sa’o’i 48 su bar saman gadojin Legas

- An bawa direbobin Tanka wa'adin kwanki biyu su janye motoccin su daga gadar Legas

- An bayar da sanarwan bayan wani taron masu ruwa da tsaki da kuma shuwagabanin hukumomin tsaro

- Mahukuttan sun bayyana cewa tsayuwar motoccin a gadar na iya sanya gadar ta karye kuma barazana ne ga tsaro

Gwamnatin jihar ta ba da wa’adin ne a wurin wani taro na masu ruwa da tsaki da ta yi a Hedkwatar Apapa, ta Sojin Ruwa na Yammacin kasa.

Taron wanda ya samu halartuwar manyan Dattawa na kasan nan da shuwagannin na Hukumomin tsaro da kuma wakilai daga kamfanoni, in da shugaban Sojin sama mai suna Abbah yace taruwar motocin a kan gadojin zai iya zama barazana ga tsaro, saboda zai iya zama wurin yin fashi a sauka ke.

An bawa direbobin tanka sa’o’i 48 su bar saman gadojin Legas
An bawa direbobin tanka sa’o’i 48 su bar saman gadojin Legas

Ya kara da cewa ana cikin yanayin kallubalen tsaro a kasar nan, saboda haka taruwar motocin a kan gadar zai saukaka yin fashi, tunda ba wanda ya san lokaci ko wurin da barayi ke kai hari. Ba wanda zai iya fadin manufar su shiyasa ba zamu iya bari a aje motocin har na tsawon mako biyu zuwa uku ba a kan gadar.

KU KARANTA: EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

A ranar Litinin hukumar Sojin Ruwa ta tura Jirgin ta mai saukar Angulu don dauko hoton wararen wanda al’amarin idan ka gani abun damuwa ne sosai. Mutane dayawa sun rasa rayukan su sakamakon wannan rufewar hanya. Gadojin anyi su ne tun shekarun 1970s wanda kuma a gina su ne don motoci su wuce a kai ba wai don sun tsaya a kai na tsawon lokaci ba, wanda hakan zai iya haddasa rushewar gadar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164