Butulci: Budurwa tayi watsi da bukatar auren saurayin da ya sadaukar da kodar sa domin ceton rayuwar ta
- Masoya Simon Louis da Mary Emmanuelle sun shafe fiye da shekaru 20 suna soyayya
- Simon ya bayar da kodar sa domin ceton rayuwar Mary lokacin da rayuwar ta ke cikin hatsarin shekawa lahira
- Ya nemi su yi aure bayan ta warke amma sai tayi watsi da bukatar sa
Masoya Simon Louis da Mary Emmanuelle sun shafe fiye da shekaru ashirin suna cin soyayya.
A yayin da suke tsaka da more soyayyar su ne sai Mary ta gamu da wata rashin lafiya dake bukatar sai an yi mata dashen koda ko kuma ta rasa ranta. Lamarin rashin lafiyar Mary ya zo da rudani kasancewar tana da wani nau'in jini mai wuyar samu, a saboda haka samun kodar da za tayi daidai da jininta ya yi wahala.
Saidai Mary ta auna arziki bayan gwaje-gwajen likitoci ya tabbatar da cewar kodar sahibinta Simon za tayi daidai da irin jininta.
Cikin doki da farinciki Simon ya sadaukar da kodar sa domin ceton rayuwar sahibar sa.
DUBA WANNAN: Yarinya mai shekaru 11 da yayanta mai shekaru 14 ya yiwa ciki ta haihu
Bayan an yi dashen kodar cikin nasara kuma dukkansu sun warke sai Simon ya bukaci Mary da suyi aure ganin dama sun dade suna soyayya. Amma abin mamaki, babu kunya sai Mary ta ki amincewa da wannan bukata ta Simon.
Simon ya shaidawa manema labarai cewar ko kadan bai yi nadamar bayar da kodar sa ga Mary ba duk bata amince da bukatar sa ta suyi aure.
A nata bangaren, Mary, ta bayyana cewar ba wai taki amincewa bane da bukatar Simon, kawai dai ta ce masa sai tayi tunani ne a kan hakan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng