'Yan sanda sunyi ram da wata kungiyar masu garkuwa da mutane a Kaduna
- Rundunar Yan Sandan Najeriya sunyi nasarar cafke wata kungiyar yan fashi da makami da satar mutane a kaduna
- An kama su yayin da sukayi yunkurin karbar kudin fansa bayan sace wata yarinya mai shekaru 9 a karamar hukumar Kauru
- Har ila yau, Yan Sandan sun cafke wani Dan Sandan boge da ya shahare wajen damfarar al'umma yana karbe musu kadade
A ranar 30 ga watan Janairun 2018 ne Rundunar Yan Sanda ta gabatar wa manema labarai wasu yan kungiyar fashi da makami da satar mutane da suka dade suna adabar al'umma a Kauru da ke jihar Kaduna wanda a kwanakin baya suka sace wata yarinya Hadiza Husseini mai shekaru 9 a duniya.
A yayin da ya ke gabatar da su ga manema labarai, Jami'in hulda da jama'a na Rundunar, CSP Jimoh Moshood ya kuma ce rundunar tayi nasarar cafke wani mutum mai suna John Torsoo wanda ya dade yana damfarar al'umma da sunan cewa shi jami'in Dan Sanda ne.
KU KARANTA: Yadda wani Soja da dansa suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da Boko Haram
'Yan kungiyar fashi da makamin da aka samu da bindigogi da alburusai daban-daban sun Shugaban Kungiyar Bello Musa (27), Musa Sani (33), Ibrahim Rere (70), Hudu Yahaya (35) da kuma Isah Aliyu (50). An cafke su ne a Unguwar Bala da ke karamar hukumar Kauru na jihar Kaduna yayin da suke kokarin karbar kudin fansa N500,000 na yarinyar da suka sace.
Shi kuma John Torsoo an kama shi ne da takardun boge na motocin da ya damfare al'umma cewa zai siyar musu, ya kabi jimlar kudi N444,000 daga wurin mutane hudu kafin jami'an sashin binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan su kama shi.
Rundunar za ta gabatar da su a kotu domin a yanke musu hukunci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng