Gwamnan jihar Kano ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa (Ibro) da kayan daki

Gwamnan jihar Kano ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa (Ibro) da kayan daki

Iyalen marigayi Rabilu Musa (Ibro)sunyi matukar godiya ga mai girma gwamnan jihar Kano. Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa ga gagarumin hidiman da yayi musu.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tallafawa Malama Jawahir Rabilu Musa, diyar shahrarren jarumin fim, marigayi Dan Ibro, da kayan daki.

Iyalen marigayin sun nuna godiyarsu ga gwamnan ne inda wasu hotuna suka bayyana na irin kayayyakin da ya taimaka musu da su.

Gwamnan jihar Kano ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa (Ibro) da kayan daki

Gwamnan jihar Kano ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa (Ibro) da kayan daki

Za'a daura auren Jawahir da Saleh Isa gobe Asabar, 20 ga watan Junairu, 2018 a garin Wudil dake jihar Kano.

KU KARANTA: An yi wa wata mata fyade, tana tsaka da jego

Marigayi Rabilu Musa Ibro babban shararren dab wasan kwaikwayo ne wanda ya rasu ranar 9 ga watan disamba na 2014.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel