Yanzu na’urar ATM za ta koma amfani da yatsun mutum – CBN

Yanzu na’urar ATM za ta koma amfani da yatsun mutum – CBN

- Za a daina amfani da lambobin sirri na FIN a na’urar ATM

- CBN tace za a koma aiki da yatsun mutum wajen cire kudi

- Mr. Dipo Fatokun ya bayyana wannan jiya a Garin Ibadan

Za ku ji mun samu labarin cewa za a koma zarar kudi ta ATM ta yatsu ba lambar FIN na sirri ba. Ko da dai hakan akwai tsada amma wani Darekta na CBN yace dole a gyara sha’anin tsaro a bankunan Kasar.

Yanzu na’urar ATM za ta koma amfani da yatsun mutum – CBN

Na’urar ATM za ta rika aiki da tambarin yatsun mutum
Source: Getty Images

Bisa dukkan alamu sai masu satar kudin Jama’a ta na’urar ATM su fara shirin canza salo don kuwa babban bankin Najeriya na CBN zai kawo karshen damfarar wasu da ake yi ta na’urar ana yin gaba da kudin su saboda ba su yi karatun zamani ba.

KU KARANTA: Buhari zai kashe Biliyan 7 wajen kula da jiragen sama

Nan gaba kadan na’urar ATM za ta koma amfani da tambarin yatsun mutum Inji wani babban Darekta na Bankin CBN Dipo Fatokun. Fatokun yace za a maye gurbin lambar da ake amfani da ita na FIN na sirri. Fatokun ya bayyana wannan ne a Garin Ibadan.

A cewar sa wasu saboda jahilci kan bada lambar tsaron su na FIN wanda wannan zai bada damar a sace masu kudi daga asusun su. Yanzu ana kokarin komawa amfani ne da irin su yatsun mutum da sauran fasaha na zamani a Kasar amma zai ci kudi Inji Darektan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel