Yan bindiga sun bindige Basaraken a ƙauyen Kanam
Wasu yan bindiga sun kai ma sarkin kauyen Gyangyang dake karamar hukumar Kanam na jihar Filato, Alhaji Mohammed Suleiman, inji rahoton kamfanin dillancin labaru.
Wata majiya daga iyalan Sarkin, yace yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, dauke da muggan makamai inda suka halaka Sarkin, bayan sun tattare hanyoyin shiga gidan duka.
KU KARANTA: Takura ma Musulmai: Gwamnatin ƙasar China ta kwace Qur’anan Musulmai don hana su karatu
“Mu dai muna barci sai muka ji karar harsashi, lokacin da muka yi kokarin fitowa daga dakunan mu, sai yan bindigan suka tare mana kofa” Inji majiyar.
Shi ma shugaban karamar hukumar Kanam, Hamidu Bale ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace “Nayi magana da da shugaban Yansandan yankin, tare da sauran hukumomin tsaro, yanzu sun mamaye unguwar.”
Sai dai da aka tambaye Kaakakin hukumar Yansandan jihar Filato, ASP Terna Tyopev yace bashi da masaniya kan faruwar lamarin, kamar yadda majiyar Legit.ng.
“Zan kira DPO dake yankin don in ji ta bakinsa.” Inji Kaakakin Yansandan, ASP Tyopev Terna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng