Ana zargin wani soja ya yiwa 'yar gudun hijira ciki
- An zargi wani sojan Najeriya da yiwa wata 'yar gudun hijira ciki
- Lamarin ya faru ne a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kan hanyar zuwa Damboa a jihar Maiduguri
Ana zargin wani soja da yiwa wata 'yar gudun hijira ciki a sansanin 'yan gudun hijira da ke kan hanyar zuwa Damboa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
A cewar mai bayar da labarai kan al'amuran jihar Borno a mai suna Dan Fulani, wanda ya kwarmata labarin a dandalin sada zumunta na Tuwita ya ce,
Sojan wanda aka boye sunansa, ya yiwa yarinyar da aka ba shi amanar kareta a sansanin ciki, a cikin wani halin na ban mamaki da tausayi.
Dan Fulani ya kuma bayyana cewa, zarge-zarge ya yi karfi kan 'yan kato da gora da aka fi sani da CJTF da ke taimakawa wajen samar da tsaro a sansanonin 'yan gudun hijira da yin lalata da 'yara mata 'yan gudun hijira a sansanoninsu a jihar duka da cewa ba a tabbatar da zarge-zargen ba.
A kwanan baya ne dai wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana yawaitar lalata da yara mata 'yan gudun hijira a sansanoninsu a jihar wanada ta kai gwamnati ta yi ikirarin gudanar da bincike.
Wasu rahotani na cewa lalacewar al'amura gami da fatara, da kuma yunwa ta sa mata na yin lalata domin su samu abinci daga hannun jami'a a sansanoninsu.
Ku biyomu a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng