AFCON 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Tuna da Super Eagles bayan Rashin Nasara a Hannun Morocco
- Gwamnatin tarayya ta yi tsokaci kan rashin nasarar da tawagar Super Eagles ta yi a hannun Atlas Lions ta kasar Morocco a gasar AFCON 2025
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a ya yaba da jarumta da kwazon da 'yan wasan suka nuna a gasar
- Mohammed Idris ya bayyana cewa kokarin da 'yan wasan suka yi ya sanya sun sa 'yan Najeriya alfahari duk da rashin nasarar da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yaba wa tawagar Super Eagles bisa jarumtarsu da ƙwazon da suka nuna a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).
Gwamnatin tarayyar ta yi yabon ne duk da rashin nasarar da suka yi a wasan kusa dana karshe da suka kara da tawagar Atlas Lions ta kasar Morocco.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya fitar wadda aka sanya a shafin X, ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Bayan Morocco ta doke Najeriya, BUA ya yi magana kan alkawarin Dalolin kudi da ya yi
Morocco ta kori Najeriya a AFCON 2025
Najeriya ta fice daga AFCON 2025 ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 bayan shan kashi a hannun Atlas Lions na Morocco a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Sakamakon da ya ba ƙasar Morocco wadda ke a Arewacin Afirka damar zuwa wasan karshe na gasar AFCON 2025.
Gwamnati tarayya ta yabawa Super Eagles
Mohammed Idris, ya ce irin wasan da Super Eagles suka yi, ya kunshi ladabi, haɗin kai da juriya, wasu dabi’u da ya ce sun yi daidai da zuciyar ’yan Najeriya.
Ya kara da cewa jajircewar tawagar tun daga farko har ƙarshe ta kasance abin alfahari ga kasar, duk kuwa da irin sakamakon da aka samu.
“Ko a cikin rashin nasara, kun nuna hali na gari, aiki tare da juriya, kuma waɗannan siffofi suna da matuƙar muhimmanci ga al’ummar da kuke wakilta."
“Ƙwallon ƙafa na da nasara da rashin nasara, amma kokarinku, jajircewarku da zuciyar faɗa da kuka nuna a duk tsawon wannan gasa sun sa ’yan Najeriya a gida da wajen kasa sun girmama ku tare da gode muku."
“Kun tunatar da mu cewa sanya kore da fari na nufin jarumtaka, haɗin kai da rashin yin kasa a gwiwa. Ku ɗaga kawunanku sama. Ku koyi darasi daga wannan karawar, ku zauna cikin haɗin kai, ku kuma dawo da karfi.”
“Najeriya na alfahari da ku, kuma tana godiya bisa farin ciki da fata da kuka ba mu a wannan gasa. Kun yi abin a yaba, Super Eagles. Al’umma tana tare da ku koyaushe."
- Mohammed Idris

Source: UGC
Morocco za ta kara da Senegal
A bugun fenaritin, mai tsaron ragar Morocco, Bounou, ya hana Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi cin kwallo bayan ya buge bugun da suka yi.
Yanzu haka Morocco za ta kara da Senegal ranar Lahadi, 18 ga watan Janairun 2026 bayan da tawagar Lions of Teranga ta doke Masar ta Mohamed Salah da ci 1-0 a wasan kusa da na ƙarshe, sakamakon kwallon da Sadio Mane ya ci.
BUA zai ba Super Eagles daloli
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshakin attajiri kuma shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya yi magana kan alkawarin da ya yi wa Super Eagles.
Abdulsamad Rabiu ya bayyana cewa zai cika alkawarin da ya yi wa tawagar Super Eagles na ba su kyautar $500,000.
Attajirin dan kasuwar ya ce zai cika wannan alkawar duk da rashin samun nasarar kaiwa ga wasan ƙarshe na lashe kofin AFCON 2025.
Asali: Legit.ng
