AFCON 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Aika Sako ga Super Eagles yayin da Take Shirin Fafatawa da Morocco
- Tawagar Super Eagles ta Najeriya na shirin fafatawa da Atlas Lions na Morocco a wasan na kusa da na karshe a gasar cin kofin Nahiyar Afrika
- Gwamnatin tarayya ta aika da sako mai muhimmanci yayin da 'yan wasan Super Eagles ke shirye-shiryen buga wasan na AFCON a yau
- Za a buga wasan ne dai a ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 a birnin Rabat na Morocco da misalin karfe 9:00 na dare a agogon Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi muhimmin kira ga ’yan wasan Super Eagles yayin da suke shirin fafatawa da kasar Morocco a gasar AFCON 2025.
Gwamnatin tarayya ta bukaci 'yan wasan Super Eagles da su buga wasan cikin kwarin gwiwa da haɗin kai a wasan na kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).

Source: UGC
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya fitar ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 a shafinsa na X.
Me gwamnati ta gayawa Super Eagles?
Miniatan ya ce daukacin ’yan Najeriya suna tare da tawagar baki ɗaya, inda ya yaba da ladabinsu, jarumtarsu da kuma irin amincewar da suka nuna tun farkon gasar.
“Yayin da kuke shirin fuskantar Morocco a wasan kusa da na karshe na AFCON, ina so ku sani cewa daukacin Najeriya tana nuna goyon baya a gare ku."
- Mohammed Idris
Ya ce irin bajintar da tawagar ta nuna zuwa yanzu ta sake tunatar da ’yan Najeriya dalilin da ya sa Super Eagles ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin kungiyoyin da aka fi girmamawa a nahiyar Afrika.
“Kun taɓa zuwa wannan mataki a baya; kun san abin da ake buƙata domin cin nasara a wannan matakin."

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
- Mohammed Idris
An yaba da kwazon 'yan Super Eagles
Ministan ya ce nasarorin da Najeriya ta samu a gasar AFCON a baya da kuma cin galaba kan manyan abokan hamayya sun samo asali ne daga aiki tare, kwarin gwiwa da kuma zuciyar gwagwarmaya.
“Waɗannan nasarori ba sa’a ba ne; sun samo asali ne daga haɗin kai, kwarin gwiwa da zuciyar gwagwarmaya, kuma kun nuna irin wannan zuciyar a wannan gasar."
- Mohammed Idris
'Yan Najeriya na goyon-bayan Super Eagles
Mohammed Idris ya kara da cewa ’yan wasan na ɗauke da burin miliyoyin ’yan Najeriya yayin da suke shiga fili domin buga wasa.
“Yayin da ku ke taka leda a fili, ku tuna ba ku kaɗai ba ne; kuna ɗauke da burin miliyoyin ’yan Najeriya."
- Mohammed Idris
Gwamnatn tarayya ta ba 'yan kwallo shawara
Ya shawarci tawagar da su buga wasan cikin kwarin gwiwar zakaru (da kuma haɗin kan ’yan’uwantaka, tare da ci gaba da nuna kishirwar samun nasara.
“Ku ci gaba da mai da hankali, ku amince da juna, ku kuma ba da iyakar kokarinku daga busar farko har zuwa ta ƙarshe."
- Mohammed Idris

Source: Twitter
Ya ce ’yan wasan sun cancanci kaiwa matakin wasan kusa da na karshe, kuma suna da kwarewar da za ta kai su gaba a gasar.
“A yau da daddare, ku fita ku rubuta wani sabon babi na alfahari a tarihin kwallon ƙafa na ƙasarmu."
“Ku buga da zuciya, ku buga da alfahari, ku buga wa Najeriya.”
- Mohammed Idris
Super Eagles za su kara da Morocco ne a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, ranar Laraba da misalin karfe 9:00 na dare agogon Najeriya.
An yi wa Super Eagles tanadin kyauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshakin attajiri, Abdulsamad Rabiu BUA ya yaba da nasarar da Najeriya ta samu kan Algeria a gasar AFCON 2025.
Babban mai kudin ya ce zai ba da $100,000 ga kowace kwallon da aka ci a wasan kusa da na karshe da kasar za ta buga da Morocco.
Hakazalika, hamshakin attajirin ya yi alkawarin ba da makudan daloli idan har 'yan wasan Super Eagles suka samu nasara a wasan karshe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

