AFCON 2025: Abin da Muka Sani game da Laryea, Alkalin Wasan Najeriya da Morocco
- Hukumar CAF ta zabi alkalin wasa, Daniel Laryea domin jagorantar babban wasan kusa da na karshe tsakanin Najeriya da Morocco
- An dauko alkalan VAR daga kasashen Afirka Ta Kudu da Tunisiya domin tabbatar da adalci biyo bayan korafe-korafen da Algeria ta shigar
- Najeriya dake takama da Victor Osimhen za ta fafata da mai masaukin baki a ranar Laraba domin neman gurbi a wasan karshe na AFCON
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Morocco - Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta tabbatar da sunayen jami’an da za su jagoranci wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin Afirka (AFCON 2025).
Wasan zai gudana ne tsakanin Super Eagles ta Najeriya da kuma mai masaukin baki, Morocco, kamar yadda wani rahoto na Legit Hausa ya nuna.

Source: Getty Images
An zabi alkalin wasan Najeriya-Morocco
Jaridar Leadership ta rahoto cewa wannan babban wasa zai gudana ne a ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2026, da ƙarfe 9:00 na dare a filin wasa na Prince Moulay Abdallah da ke birnin Rabat.
Alƙalin wasa ɗan ƙasar Ghana, Daniel Nii Ayi Laryea, wanda ake gani a matsayin ɗaya daga cikin gogaggun alƙalai a nahiyar, shi ne zai busa wasan.
Zai samu taimakon Zakhele Thusi Granville Siwela daga Afirka Ta Kudu da Souru Phatsoane daga Lesotho a matsayin mataimaka.
Haka kuma, an zaɓi Abongile Tom daga Afirka Ta Kudu don ya jagoranci na’urar nan mai taimaka wa alƙali wato VAR.
Wanene Laryea, alkalin wasan Najeriya?
Wani rahoto da aka wallafa a shafin WikiPedia ya nuna cewa, an haifi Daniel Nii Ayi Laryea a ranar 11 ga Satumba, 1987, kuma ya zama alkalin wasa na kasa da kasa karkashin FIFA a 2014.
Rahoton ya nuna cewa Laryea ya kasance daya daga cikin alkalin gasar firimiyar Gahana, sannan a 2021, aka zabe shi ya zama alkali a gasar zakarun nahiyar Afrika (ANC) a Kamaru.
Laryea ne ya busa wasan karshe na kofin Ghanaian FA Cup tsakanin kungiyar Hearts of Oak da Ashanti Gold. An ce tun yana dan shekara 17 a 2005 ne ya fara alkalancin wasanni a Ghana.

Kara karanta wannan
AFCON2025: Najeriya ta gamu da babban cikas yayin da take shirin haduwa da Moroko

Source: Twitter
Korafe-korafe kan busan alkalan AFCON
Nadin Laryea na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ido sosai kan yadda alƙalai ke gudanar da wasanni a wannan gasa ta cin kofin nahiyar Afrika ta 2025.
Bayan da Najeriya ta doke Algeria a wasan kusa da na kusa da na ƙarshe, hukumar ƙwallon ƙafar Algeria ta shigar da ƙara gaban hukumar CAF da FIFA tana zargin rashin adalcin alƙali.
Sai dai, CAF ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan dukkan wasannin da aka yi na matakin kusa da na kusa da na ƙarshe don tabbatar da cewa ba a samu son kai ba.
Hukumar ta sake jaddada cewa za ta hukunta duk wani ɗan wasa, jami'i, ko ɗan jarida da aka samu da laifin tada zaune tsaye ko rashin tarbiyya a yayin gasar, cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin CAP.
Najeriya ta gamu da cikas a AFCON 2025

Kara karanta wannan
'Yan wasan Najeriya sun tumurmusa Algeria, sun tsallaka zuwa mataki na gaba a AFCON
A wani labari, mun ruwaito cewa, kyaftin ɗin Super Eagles kuma babban ɗan wasan tsakiya, Wilfred Ndidi, ba zai buga wasan kusa da na ƙarshe da za su fafata da ƙasar Morocco ba.
Ndidi ya samu dakatarwar wasa ɗaya ne sakamakon tara katin gargadi guda biyu (yellow cards) a lokacin wasannin Najeriya da suka gabata.
Duk da haka, Victor Osimhen ya sha alwashin cewa Najeriya za ta lallasa Morocco mai masaukin baki domin kai wa wasan karshe na gasar AFCON 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
