Sababbin Matasan 'Yan Wasa 5 da Suka Dauki Hankula a Gasar AFCON 2025

Sababbin Matasan 'Yan Wasa 5 da Suka Dauki Hankula a Gasar AFCON 2025

Kasar Morocco - Ana ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da ake gudanarwa a kasar Morocco.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

A ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 za a buga wasannin zagayen dab da na kusa da karshe tsakanin kasashe hudu da suka rage a gasar.

'Yan wasan da suka nuna bajinta a AFCON 2025
Dan wasan Najeriya, Akor Adams, dan wasan Cameroon, Christian Kofane da dan wasan Morocco, Ibrahim Diaz Hoto: @akorjeromeadams, @talentScout, @Beejaysport
Source: Twitter

'Yan wasan da suka dauki hankali a AFCON 2025

Legit Hausa ta tattaro matasan 'yan wasan da suka nuna hazaka wajen wakiltar kasashensu a gasar AFCON 2025.

Wadannan zaratan 'yan wasa sun taka rawar gani a wasannin da suka buga yayin da suke wakiltar kasashensu.

Ga jerinsu a nan kasa:

1. Ibrahim Díaz (Morocco)

’Yan Morocco da dama sun sa rai ne ga kyaftin Achraf Hakimi, amma yayin da yake murmurewa daga rauni kuma bai taka rawar gani sosai ba a matakin rukuni, Ibrahim Diaz ya zama sabon gwarzonsu.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Kocin Morocco ya fadi sunayen 'yan wasan Najeriya 3 da yake tsoro

'Dan wasan na gaba a Real Madrid, Ibrahim Díaz ya nuna ba da wasa ya zo ba wajen wakiltar Morocco a gasar AFCON 2025.

Ibrahim Diaz ya taka rawar gani a wasannin da Morocco ta buga a AFCON 2025
Dan wasan gaba na kasar Morocco, Ibrahim Diaz Hoto: @ALMAGHRIB1956
Source: Twitter

Ibrahim Díaz mai shekaru 26 ya ci kwallo a dukkan wasannin da ya buga, ciki har da kwallon da ta ba Morocco nasara a kan Tanzania a zagaye na 16.

Hakazalika ya zura kwallo a wasan dab da na kusa da na karshe wanda Morocco ta buga da kasar Cameroon.

An haife shi a Malaga, Spain, kuma ya taba wakiltar Spain a 2021 kafin daga bisani ya koma buga wa Morocco wasa, kasar mahaifinsa, tashar Beinsports ta kawo rahoton.

Tsohon ɗan wasan na Manchester City da AC Milan zai taka muhimmiyar rawa yayin da Morocco za ta kara da Najeriya a ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 a wasan dab da na kusa da na karshe.

2. Christian Kofane (Cameroon)

Duk da rikice-rikicen da ke yawan addabar kungiyar Cameroon, sun nuna bajinta AFCON 2025, musamman ta hannun matasan ’yan wasa.

Daga cikinsu akwai Christian Kofane, ɗan wasan gaba mai shekaru 19 daga birnin Douala.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Morocco ta gamu da babbar matsala tana shirin karawa da Najeriya

Christian Kofane ya yi kokari a wasannin Cameroon
Dan wasan Cameroon, Christian Kofane Hoto: @OneFootball
Source: Twitter

Shafin cafonline ya ce Christian Kofane, wanda ya koma Bayer Leverkusen daga Albacete (Spain) kafin fara kakar wasanni ta bana, ya buga wasanni 10 a Jamus, inda ya ci kwallo a gasar Bundesliga da kuma Champions League.

Wannan ne ya sa kocin Cameroon, David Pagou, ya gayyace shi domin taka leda a gasar AFCON 2025.

Ya ci kwallon nasara a kan Mozambique a wasan rukuni, sannan ya sake cin kwallo a wasan da Cameroon ta doke Afirka ta Kudu da 2–1 a zagaye na 16.

3. Ibrahim Mbaye (Senegal)

Matashin ɗan wasan gaba na Paris Saint-Germain, mai shekaru 17, ya taso ne a Faransa kuma ya taba wakiltar Faransa a matakin matasa.

Amma kafin fara gasar AFCON 2025, ya yanke shawarar wakiltar Senegal, kasar mahaifinsa.

Ibrahim Mbaye ya yi bajinta a wasannin da Cameroon ta buga a AFCON 2025
Ibrahim Mbaye yayin da yake takawa kasar Cameroon leda Hoto: @Ligue1_ENG
Source: Twitter

Ibrahim Mbaye, wanda ya bugawa PSG wasanni 20 a wannan kakar, ya nuna cewa ya cancanci taka leda tare da taurari irin su Sadio Mané.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: An fadawa Najeriya abin da za ta yi don doke Morocco a 'semi finals'

Ya bayar da kwallo a wasan da aka ta tashi 1–1 da DR Congo, sannan ya sake taimakawa a wasan Benin.

Shafin Foot Africa ya ce a wasan zagaye na 16, Ibrahim Mbaye ya ci kwallo a nasarar da Senagal ta samu ta 3–1 a kan Sudan.

4. Ibrahim Maza (Algeria)

Ana masa lakabi da “Mazadona”, kuma ya kasance tauraro a tafiyar Algeria zuwa matakin dab da na kusa da na karshe.

Ibrahim Maza mai shekaru 20 an haife shi a Berlin, ya taba wakiltar Jamus a matakin matasa kafin ya koma bugawa Algeria wasa a 2024, shafin onefootball.com ya tabbatar da hakan.

Ibrahim Maza ya takawa Algeria leda a gasar AFCON 2025
Dan wasan tsakiya na Algeria, Ibrahim Maza Hoto: @OnzeMundial
Source: Twitter

Dan wasan na tsakiya, wanda Leverkusen ta siya kan kusan €12m, ya ci kwallo bayan ya shigo daga benci a wasan farko da Sudan.

Hakazalika ya ci gaba da taka rawar gani, inda ya zama gwarzon wasa a kan Burkina Faso kuma ya ci kwallo a kan Equatorial Guinea.

5. Akor Adams (Nigeria)

Babban ɗan wasan gaba mai shekaru 25 ya kara ƙarfi ga tawagar Super Eagles ta Najeriya wadda Victor Osimhen da Ademola Lookman ke jagoranta.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Abin da muka sani game da Laryea, alkalin wasan Najeriya da Morocco

Akor Adams ya zura kwallaye a wasannin Najeriya a AFCON 2025
Dan wasan gaba na Najeriya, Akor Adams Hoto: @akorjeromeadams
Source: Twitter

Akor Adams, wanda ya koma Sevilla daga Montpellier, ya fara buga wa Najeriya wasa ne a Oktoba inda ya ci kwallo a wasansa na farko.

A gasar AFCON 2025, ya nuna bajinta a wasan da Najeriya ta doke Mozambique da 4–0, a zagaye na 16, inda ya ci kwallo guda kuma ya bayar da taimako aka zura kwallo.

Hakazalika, Akor Adams ya zura kwallo a ragar Algeria a wasan zagayen dab da na kusa da na karshe.

'Yan wasan Najeriya sun yi bore a AFCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan wasan Super Eagles na Najeriya da masu horaswa sun yi bore a gasar AFCON 2025.

'Yan wasan sun dauki matakin tafiya zuwa birnin Marrakech don buga wasa na gaba da nufin nuna fushinsu bisa rashin biyansu hakkoki da alawus-alawus.

Hakan ya faru ne sakamakon kin biya yan wasa alawus-alawus na wasanni huɗun da aka buga a gasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng