AFCON: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Jika 'Yan Wasan Najeriya da Kudade Masu Nauyi

AFCON: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Jika 'Yan Wasan Najeriya da Kudade Masu Nauyi

  • Gwamnatin Najeriya ta fara tura alawus na wasannin gasar AFCON a asusun yan wasa da masu horarsawa a tawagar Super Eagles
  • Hakan ya biyo bayan barazanar yajin aikin da 'yan wasan suka yi saboda rashin biyansu alawus na wasanni hudu da suka samu nasara
  • Karamar Ministar Kudi, Misis Doris Uzoka-Anite ta ce gwamnati ta bullo da wani tsari da zai magance sake samun jinkirin biyan kudaden nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ta fara biyan dukkan bashin alawus-alawus na wasanni da ’yan wasan Super Eagles suke bi a gasar cin kofin Afirka (AFCON).

Wannan dai ya biyo bayan barazanar da 'yan wasa da masu horar da Super Eagles suka yi cewa ba za su fita atisaye ko tafiya filin da za su kara da Algeria ba matukar ba a biya su alawus dinsu ba.

Kara karanta wannan

AFCON: 'Yan wasan Najeriya sun yi bore, sun gindaya sharadi kafin buga wasa da Algeria

Tawagar Super Eagles.
Tawagar Super Eagles a cikin filin wasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @SuperEagles
Source: Twitter

An fara biyan alawus ga tawagar Najeriya

Karamar Ministar Ma’aikatar Kuɗi, Mrs Doris Uzoka-Anite, ce ta tabbatar da cewa an biya hakkokin 'yan wasan, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a safiyar ranar Alhamis.

Ta ce Gwamnatin Tarayya da haɗin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN), ta shawo kan matsalolin da suka janyo jinkiri wajen canjin kuɗaɗen waje domin tabbatar da cewa ’yan wasan sun samu hakkinsu ba tare da ƙarin jinkiri ba.

“Ina farin cikin sanar da ci gaban da aka samu dangane da biyan alawus ɗin wasannin Super Eagles a gasar AFCON 2025.
"Gwamnatin Tarayya da CBN sun daidaita tsarin musayar kuɗi yadda za a biya ’yan wasan cikin gaggawa," in ji ta.

Gwamnatin tarayya ta ji koken Super Eagles

A cewarta, an fitar da dukkan alawus na wasannin rukuni gaba ɗaya kuma sun kammala bin matakan doka, yayin da ake ci gaba da tura kuɗaɗen zuwa asusun ’yan wasan.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

Wannan sanarwa ta biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa ’yan wasan Super Eagles sun yi barazanar ƙin tafiya Marrakech domin buga wasan daf da na kusa da na ƙarshe da Algeria, muddin ba a biya su alawus ɗin nasarorin da suka samu ba.

Ministar ta bayyana cewa gwamnati ta bullo da tsarin da zai hanzarta musayar Naira zuwa kuɗaɗen waje, domin biyan bukatar ’yan wasan da ke son a biya su da kuɗin ƙetare.

Doris Uzoka-Anite.
Karamar Ministar Kudi ta Najeriya, Misis Doris Uzoka-Anite tana tsakiyar aiki a ofis a Abuja Hoto: Doris Uzoka-Anite
Source: Twitter
“Mun samar da tsarin gaggawa domin mayar da Naira zuwa kudin waje, bisa ga abin da ’yan wasan ke so,” in ji ta.

Minista ta fadi matakin da aka dauka

Uzoka-Anite ta kuma tabbatar da cewa an ɗauki matakai domin hana sake samun irin wannan jinkiri nan gaba, inda ta ce za a sauƙaƙe tsarin biyan alawus ɗin ’yan wasa bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Ta jaddada cewa gwamnatin tarayya na da cikakken ƙuduri wajen kula da walwalar tawagar ƙasa, domin su ci gaba da taka rawar gani yayin da gasar ke shiga matakan ƙarshe, in ji Leadership.

Ndidi ya zama sabon Kyaftin na Super Eagles

A wani labarin, kun ji cewa tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya ta samu sabon kyaftin bayan ritayar Ahmed Musa da Williams Troost Ekong.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya hango abin da zai wargaza jam'iyya, ya bada shawara tun wuri

An tabbatar da nadin dan wasan tsakiya na kungiyar Beşiktaş, Wilfred Ndidi, a matsayin sabon kyaftin din tawagar Super Eagles.

Wilfred Ndidi mai shekara 29 ya karɓi ragamar jagoranci na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafi nasara a Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262