AFCON 2025: An Saka Kudi ga 'Yan Super Eagles kan Zura Kwallo a Wasansu da Mozambique
- Gwamnatin Tarayya ta yi wa Super Eagles alkawarin $10,000, wato kusan Naira miliyan 14, kan kowace kwallo da za su ci a wasan da za su fafata da Mozambique
- Super Eagles za ta kara da tawagar Mambas ta Mozambique a wasan zagaye na 16 na gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) 2025 a ranar Litinin, 5 ga Janairun 2026
- 'Yan kwallon Super Eagles sun kammala wasannin rukuni na gasar da cikakkiyar nasara, inda suka lashe dukkan wasanninsu tare da cin kwallaye takwas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tawagar Super Eagles ta samu gagarumin karin karfafa gwiwa gabanin wasan da za ta fafata da Mambas na Mozambique.
Gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar masu zaman kansu, ta sanya alawus mai tsoka kan duk wata kwallo da za a ci a wasan.

Source: Getty Images
Jaridar Leadership ta ce Shugaban hukumar wasanni ta kasa (NSC), Malam Shehu Dikko, ne ya tabbatar da wannan tsari.
Najeriya za ta fafata da Mozambique a daren Litinin, 5 ga watan Janairun 2026 a filin wasa na Stade de Fès.
Wace kyauta za a ba Super Eagles?
Kowace kwallo da Super Eagles suka ci za ta zo da ladan Naira miliyan 14, lamarin da ke kara ƙarfafa kwarin gwiwa kan tafiyar Najeriya a AFCON 2025.
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ba wa Super Eagles $10,000 kan kowace kwallo da za su ci a wannan wasan na zagaye na bugin kifa daya kwala.
Malam Shehu Dikko ya bayyana cewa wannan adadi ya ninka dala dubu biyar ($5,000) da aka rika biya kan kowace kwallo a wasannin rukuni.
Dalilin yiwa 'yan wasan alkawarin miliyoyi
A cewarsa, matakin na daga cikin dabarun da gwamnati ke bi domin ƙarfafa gwiwar ‘yan wasan Super Eagles gaba ɗaya, tare da kawar da duk wata tangarda yayin da Najeriya ke kokarin lashe kofinta na huɗu na AFCON a Morocco.
“Mun shirya Super Eagles gaba ɗaya domin su yi nasara a wannan gasa. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sakin kudin AFCON."

Kara karanta wannan
Bayan ya fadi wasu kalamai, Man United ta kori kocinta, ta maye gurbinsa nan take
"Kuma abokan haɗin gwiwarmu sun kara ladan kowace kwallo zuwa dala 10,000 a matakin bugun kifa daya kwala. Wannan alawus zai ci gaba da karuwa yayin da gasar ke ci gaba."
- Malam Shehu Dikko
Najeriya na abin kirki a AFCON 2026
Rahoton WhoScored ya nuna cewa Najeriya ta ci kwallaye takwas a wasannin rukuni, lamarin da ya sanya wannan alawus ya zama mai armashi sosai ga ‘yan wasa.
‘Yan wasan da Eric Chelle ke jagoranta sun shiga matakin bugun kifa daya kwala a matsayin ɗaya daga cikin kungiyoyin da suka fi nuna bajinta a gasar.

Source: Getty Images
Najeriya ta lashe dukkan wasannin rukunin C, inda ta doke, Tanzania da ci 2–1, Tunisia da ci 3–2 da Uganda da ci 3–1. Hakan ya ba ta maki tara cif-cif.
Tarihin kokarin Super Eagles na baya-bayan nan
Hukumar CAF ta bayyana cewa wannan ne karon farko tun 2021 da Najeriya ta lashe dukkan wasannin rukuni a AFCON, kuma karo na huɗu kenan a tarihin kasar.
Kwallaye takwas da Super Eagles suka ci a wannan mataki su ne mafi yawa da suka taba ci a zagayen farko na AFCON.
Nasarar da suka samu kan Uganda kuma ta zama nasara ta 61 a tarihin AFCON ga Najeriya, inda suka rage nasara guda ɗaya kacal su kai Masar, wadda ke kan gaba a tarihin gasar.
Super Eagles ta yi sabon kyaftin
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu sabon kyaftin bayan ritayar Ahmed Musa wanda yanzu yake buga wa Kano Pillars.
'Dan wasan tsakiya na kungiyar Beşiktaş, Wilfred Ndidi, ya zama sabon kyaftin din tawagar Super Eagles, ya gaji tsohon 'dan wasan gaban na kungiyar Leicester.
Naɗin Ndidi ya zo ne bayan ritayar William Troost-Ekong, wanda ya kasance kyaftin din rikon ƙwarya, da kuma Ahmed Musa, wanda shi ne jagoran ƙungiyar a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

