'Congo Ta Yi Tsafi ta Fitar da Najeriya a Neman Gurbin Kofin Duniya,' Kocin Super Eagles
- Kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya zargi DR Congo da yin tsafi yayin bugun fenariti a wasan neman gurbin gasar cin Kofin Duniya ta 2026
- Chelle ya ce ya ga wani a jikin bencin kasar DR Congo yana amfani da wani ruwa domin yi wa ’yan Najeriya tsafi a karshen wasan
- DR Congo ce ta yi nasara a fenariti bayan wasan ya tashi 1–1, lamarin da ya kara dagula rashin sa’ar Najeriya a neman gurbin Kofin Duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rikici ya barke a karshen wasan neman gurbin gasar kofin duniya na 2026 tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Hakan na zuwa ne yayin da kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya fito fili ya zargi abokan karawarsu da amfani da tsafi a bugun fenariti.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan zargin ne a wani sako da dan jarida mai sharhi kan wasanni, Fabrizio Romano ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda kocin Najeriya ya tayar da kura
Lamarin ya fara daukar hankali tun bayan da aka ga Chelle ya nufi wajen masu horar da 'yan wasan DR Congo bayan kammala fenaritin tare da nuna fushi ga kocin su, Sébastien Desabre.
Vanguard ta rahoto cewa an ga jami’an Najeriya suna rike shi domin kada lamarin ya rikide zuwa wani sabon rikici a filin wasa.
A yayin taron ’yan jarida bayan wasa, Chelle ya bayyana cewa abin da ya tayar masa da hankali shi ne ganin cewa akwai wani daga cikin 'yan DR Congo yana wani abu kamar sihiri.
Zargin tsafi a lokacin bugun fenariti
Kocin Najeriya, Chelle ya yi zargin cewa an yi wa 'yan Super Eagles sihiri a duk lokacin da ake shirin bugun fenariti.
Ya ce akwai wani mutum daga cikin kwamitin fasaha na DR Congo da yake amfani da wani ruwa domin ya jefa tsoro ko tangarda ga masu bugawa daga bangaren Najeriya.
Chelle ya ce wannan abin ya sa ya fusata matuka domin ya ga yana maimaita hakan kusan duk lokacin da aka sa dan Najeriya ya buga fenariti.
A kalamansa:
“A duk lokacin da ake bugun fenariti, mutumin Congo yana yin wani irin tsafi. Wannan ne ya sa na fusata, na nufe shi.”
Yadda wasan ya kaya kafin rikicin
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ce ta fara cin kwallo 'yan mintuna da fara wasan ta hannun Frank Onyeka.
Sai dai dan DR Congo Meschak Elia ya ci Najeriya kwallon da ta daidaita sakamakon a rabin lokaci na farko.

Source: Getty Images
Bayan haka babu wani kwallo da ya shiga raga har zuwa karin lokaci, wanda hakan ya kai wasan zuwa bugun fenariti bayan mintuna 120 da ci 1–1.
DR Congo ta samu nasara a fenaritin, inda Chancel Mbemba ya zura bugun karshe wanda ya raba gardama.
Wannan nasara ta ba DR Congo damar cigaba zuwa matakin karshe, yayin da Najeriya ta sake jin kunya a wani muhimmin yunkuri na neman samun gurbin buga gasar kofin duniya.

Kara karanta wannan
Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara
Matan Najeriya sun lashe WAFCON
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kwallon Najeriya mata sun lashe kofin zakarun Afrika na WAFCON na 2025.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed https://x.com/MobilePunch/status/1976384340193132744?t=3RY2i9-ryTOvKnx4oMry7Q&s=19Tinubu ya yaba wa matan bisa kokarin da suka yi tare da musu alkawura.
Bola Tinubu ya bayyana cewa bai kalli wasan ba a karon farko saboda jin tsoron hawan jini idan aka sha Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

