Abin da Katsina United Ta ce kan Zargin Yanka Makogoron ’Dan Wasan Barau FC
- Ƙungiyar Katsina United tayi karin haske kan rahoton da ke yawo cewa sun mamaye filin wasansu da Barau FC
- Katsina United ta karyata rahoton da ke cewa magoya bayanta sun yanka makogoron dan wasan Barau FC
- Ta ce labarin da aka wallafa “ƙarya da yaudara,” tana mai cewa an samu tsaro da kulawa har zuwa ƙarshen wasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta nesanta kanta daga wani rahoto da ke yawo a yanar gizo game da abin da ya faru yayin gasar Firimiya.
An gudanar da wasan tsakaninsu da Barau FC a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, a cikin gasar NPFL da aka buga.

Source: Facebook
Katsina United ta karyata kashe dan Barau FC
Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar, Nasir Gide, ya fitar ranar Lahadi 9 ga watan Nuwambar 2025 a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara wanda ka iya jawo tashin hankali.
Rahoton ya yi zargin cewa magoya bayan Katsina United sun mamaye fili, an samu rikici, har ma aka ce an yanka wani ɗan wasa.
Gide ya ce:
“Wannan ƙarya ce tsantsa, an ƙirƙira ne don ɓata sunan ƙungiyarmu da kuma harkar ƙwallon ƙafa a jihar Katsina.”
Ya jaddada cewa babu wani magoyin bayansu da ya shiga fili yayin wasan, duk da cewa an samu ce-ce-ku-ce kan hukuncin alkalin wasa.
Ya ce jami’an tsaro sun kasance cikin shiri kuma sun tabbatar da cewa an gudanar da wasan cikin kwanciyar hankali da tsari.
“Wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne, wasan ya gudana cikin tsafta da cikakken tsaro."
- Nasir Gide

Source: Original
Katsina United ta nuna takaici kan yada karya
Ƙungiyar ta nuna takaici cewa manyan jaridu suna ya wallafa irin wannan labari ba tare da tabbatar da gaskiyar abin da ya faru ba.
Ta ce irin wannan ƙarya na iya lalata sunan ƙungiyar da kuma jinkirta ci gaban ƙwallon ƙafa a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
Ƙungiyar ta kuma zargi Barau FC da ƙara yadawa da faɗaɗa wannan labari na ƙarya don neman cusa rikici tsakanin magoya baya.
Gargadin Katsina United ga masu yada karya
A cewar Gide, ƙungiyar ta umarci gidan yanar gizon da ya wallafa labarin da ya janye shi tare da bayar da haƙuri a bainar jama’a.
Ya ce idan ba su janye labarin ba, za su ɗauki matakin shari’a don kare mutuncin ƙungiyar da harkar ƙwallon ƙafa a Katsina.
Ya ce:
“Mun gargaɗi masu wallafa wannan labari su gyara shi nan da nan, in ba haka ba, za mu nemi adalci ta hanyoyin doka."
An ci taran Kano Pillar kan ta da hankali
Mun ba ku labarin cewa hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasa (NPFL) ta yi hukunci mai tsaurai a kan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
Wannan ya biyo bayan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars a wasan karshen mako da aka yi a jihar Kano.
An tashi kowa da ci 1-1, lamarin da bai yi wa wasu daga cikin magoya bayan Pillars dadi ba har ta kai ga tayar da hatsaniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


