NPFL Ta Lafta wa Kano Pillars Tara Mai Nauyi bayan Rikicin Wasa da Shooting Stars
- Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasa (NPFL) ta yi hukunci mai tsaurai a kan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
- Wannan ya biyo bayan wasan da da kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars a yammacin ranar Lahadi a jihar Kano
- An tashi kowa da ci 1-1, lamarin da bai yi wa wasu daga cikin magoya bayan Pillars dadi ba har ta kai ga tayar da hatsaniya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nigeria Premier Football League (NPFL) ta kakabawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars hukunci mai nauyi.
Wannan ya biyo bayan rikici da tashin hankali da ya faru a wasan gida da suka buga da Shooting Stars Sports Club (3SC) a ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, 2025, a filin wasan Sani Abacha da ke Kano.

Source: Facebook
AIT ta wallafa cewa a cikin sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Jami’in gudanarwa na NPFL, Davidson Owumi, hukumar ta ce an samu Kano Pillars da laifin karya dokoki da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NPFL ta hukunta kungiyar Kano Pillars
Daily Post ta wallafa cewa daga cikin laifufuffukan da NPFL ta kama Kano Pillars da su akwai rashin samar da isasshen tsaro da gaza daidaita magoya baya.
Sauran sun hada da jefa abubuwa masu haɗari a filin wasa da kuma cin zarafin ‘yan wasan ƙungiyar baƙi da jami’an wasa.
Saboda haka, hukumar ta dauki hukuncin kakaba wa Kano Pillars tarar kudi N9.5m da kuma karin wasu matakan.
Hukuncin da NPFL ta yanke wa Kano Pillars
Hukumar NPFL ta umarci Kano Pillars da ta biya tarar ₦1,000,000 na rashin samar da isasshen tsaro, ₦1,000,000 na jefa abubuwa masu haɗari a filin wasa da ₦1,000,000 na gaza daidaita dabi’ar magoya bayanta.
Kungiyar za ta kuma biya ₦1,000,000 na aikata abubuwan da suka tauye kimar wasan, sai ₦2,000,000 na cin zarafin ‘yan wasan baƙi da jami’an wasa da ₦2,000,000 na biyan diyya don jinya da lahani ga ‘yan wasa.

Source: Facebook
Bugu da kari sai kuma karin ₦1,500,000 da Kano Pillars za ta biya ƙarin diyya ga jami’an wasan, sannan an rage maki uku da ƙwallaye uku daga jadawalin ƙungiyar, haka zalika, an rufe filin wasan Sani Abacha.
Hukumar ta umarci Pillars su koma Katsina domin buga wasannin gida har zuwa ƙarshen kakar ko kuma aƙalla wasanni goma.
Kano Pillars: Ahmed Musa ya ba da hakuri
A baya, mun wallafa cewa Ahmad Musa ya fito ya ba duniya hakurin danyen aikin da magoya bayan Kano Pillars suka yi a makon jiya.
A matsayinsa Manajan kungiyar, tsohon kyaftin din na Super Eagles ya yi Allah wadai da yadda masoya suka koma ringima a filin wasa.
Tauraron ya yarda cewa babu gurbin irin wannan tashin-tashina a wajen kwallo, ya sha alwashin hada-kai da hukuma domin hukunta kungiyarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

