Dembele Ya Kafa Tarihi bayan Doke Yamal a Kyautar Ballon d'Or 2025
- Ousmane Dembele ya lashe kyautar zakaran dan kwallon duniya na maza watau Ballon d'Or 2025 a karon farko a tarihinsa
- 'Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG ya samu wannan nasara ne bayan doke matashin dan Barcelona, Lamine Yamal
- Dembele ya samu nasararo da dama a kakar wasan da ta gabata sakamakon bajintar zura kwallo, taimakawa da sauransu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da ƙkullum
France - Ɗan wasan gaba na kungiyar Paris Saint-Germain (PSG), Ousmane Dembele, ya lashe kyautar Ballon d’Or a karon farko a tarihi.
Fitaccen dan wasan ya lashe wannan kyauta ta Ballon d'Or, watau zakaran dan wasan da ya fi kowane kokari a maza a kakar wasan da ta gabata.

Source: Getty Images
Fabrizio Romano, fitaccen dan jarida mai kawo rahotanni kwallon kafa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook a daren yau Litinin.

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin Dembele a kakar wasan 2024/2025
'Dan wasan mai shekara 28 ya zura kwallaye 35 tare da taimaka wajen cin kwallaye 16 a wasa 53 a kakar da ta gabata.
Dembele ya taimakawa kungiyar PSG ta lashe manyan kofuna uku ciki har da gasar zakarun nahiyar turai watau Champions League karo na farko a tarihin kulob din.
Tauraron dan wasan, dan asalin kasar Faransan ya kuma zama ɗaya daga cikin wadanda suka fi jefa kwallaye a raga a Ligue 1, inda ya ci kwallaye 21.
Sannan an zaɓe shi a matsayin zakakurin dan wasan shekara a gasar Ligue 1 ta Faransa, kuma aka ba shi kyautar gwarzon 'dan wasan zakarun Turai.
Yadda Dembele ya zama zakaran 2025
Dembele ya doke matashin ɗan wasan Barcelona mai shekara 18, Lamine Yamal, wanda ya zo na biyu tare da lashe Kopa Trophy, kyautar zakaran matashin dan kwallon da ya fi nuna bajinta.
'Dan wasan PSG, Vitinha, ya zo na uku, yayin da dan wasan gaba na kungiyar Liverpool ta kasar Ingila, Mohamed Salah, ya zo na hudu.
Cole Palmer na Chelsea ya zo na takwas. A bana Rodri na Manchester City bai shiga jerin sunayen ba sakamakon jinya a kakar da ta gabata.

Source: Facebook
Takaitaccen jawabin da Dembele ya yi
Dembele, wanda ke jinyar rauni a halin yanzu, ya halarci bikin bayar da kyautar a birnin Paris, sai dai hawaye ya zuba daga idanunsa yayin da ya daga kyautar tasa ta tarihi, in ji rahoton Sky Sport.
“Mahaifiyata, ina so na gode miki, kin kasance tare da ni koyaushe, mama, ki na gefe na a kowane lokaci.”
“Ga iyalina, mun fuskanci abubuwa da dama tare. Mun sha wuya tare, mun yi farin ciki tare. Za mu kasance tare koyaushe.”
- In ji Dembele bayan ya jarbi kambun.
Malami ya yi hasashen nasarar Arsenal
A wani labarin, kun ji cewa Malamin coci, Joel Atuma ya yi hasashen cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta kai wasan karshe a Champion na bana.
Malamin ya ce Arsenal za ta doke PSG a wasan kusa da karshe sannan ta fafata da Barcelona a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
Ya kuma kara da cewa a iya abin da ya hango, Arsenal za ta doka Barcelona ta daukin kofin a wannan kakar wasa da ake ciki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

