Gaskiya Ta Fito kan Rahoton Ahmed Musa Ya Raba Tsala Tsalan Motoci a Kano Pillars

Gaskiya Ta Fito kan Rahoton Ahmed Musa Ya Raba Tsala Tsalan Motoci a Kano Pillars

  • Dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa ya karyata rade-radin cewa ya raba motoci masu tsada ga 'yan wasan Kano Pillars bayan nada shi shugaba
  • Ahmed Musa ya bayyana hakan da labarin karya kuma jama'a su daina yada labaran da ba a tantance ba
  • Musa ya ce burinsa shi ne gyara kungiyar Kano Pillars da gina tawaga mai karfi da zai kai ga nasara a Najeriya da Afirka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya yi martani kan rahoton cewa ya raba motoci ga yan Kano Pillars.

Ahmed Musa ya karyata rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya bai wa ’yan wasan Kano Pillars da jami’ai motoci masu tsada.

Ahmed Musa ya magantu kan rahoton raba motoci
Ahmed Musa ya karyata raba motoci ga yan Kano Pillars. Hoto: Ahmed Musa, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Ahmed Musa ya magantu kan raba motoci

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, dan wasan Super Eagles ya karyata rahotannin da ke yawo, yana mai bayyana su a matsayin karya da ruɗu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rahoton na zuwa ne bayan nadinsa a matsayin babban manajan kungiyar wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ba shi.

Jituwar da ta karade intanet a baya ta yi zargin cewa Musa ya bai wa kowane ɗan wasa da jami’in koyarwa sabbin motoci kirar 'Land Cruiser' domin bikin dawowarsa.

Da yake mayar da martani, Musa ya ce labarin ƙirƙirarre ne gaba ɗaya kuma ya roƙi jama'a da 'yan jarida su rika tantance gaskiyar labarai kafin yadawa.

Ya ce:

"Na samu labarin cewa ana yaɗa ƙarya cewa na raba motoci ga ’yan wasa da jami’an kulob bayan nada ni a matsayin manaja."
"Wannan zargin ba gaskiya ba ne kwata-kwata."
"Na roƙi jama’a, kafofin watsa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta su dinga tabbatar da sahihancin bayanai kafin yadawa."
Ahmed Musa ya ƙaryata raba motoci a Kano Pillars
Ahmed Musa ya shawarci jama'a bayan rahoton raba motoci a Kano Pillars. Hoto: Ahmed Musa MON.
Source: Getty Images

Burin Ahmed Musa game da Kano Pillars

Ahmed Musa ya kammala da cewa babban burinsa shine farfaɗo da kungiyar Kano Pillars domin ta dawo darajarta a matsayin zakara.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta saka lokacin wargajewar hadakar ADC

"Burinmu shi ne gina tawaga mai ƙarfi, ladabi da nasara, nagode da goyon baya da fahimtar ku."

- Cewar Ahmed Musa

Binciken gaskiya da aka ya an gano cewa hotunan motocin Land Cruiser da ake danganta da Musa sun samo asali ne daga wani labari daban.

A ganawar farko da ya yi da hukumar kulob din Kano Pillar bayana nada shi mukami, ya yi alkawarin dawo da martabar Pillars a kwallon kafa ta Najeriya da Afirka.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai, tsara tsare-tsare da kuma jajircewa daga dukkan masu ruwa da tsaki domin kawo sabon salo karkashin shugabancinsa.

Abba Kabir yaba Ahmed Musa mukami

Kun ji cewa gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ahmed Musa matsayin Manajan Kano Pillars, tare da kafa sabon kwamitin gudanarwa don inganta ƙungiyar.

An sake naɗa yawancin mambobin kwamitin da ya gabata, domin ƙarfafa ƙungiyar kafin a fara kakar Firimiyar Najeriya (NPL) mai zuwa.

Gwamnatin Abba na sa ran nadin Ahmed Musa zai kawo ci gaba a taka ledar 'yan wasa da kuma jawo hankalin duniya ga Kano Pillars.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel