Osimhen: An Ji Biliyoyin Naira da Man United za Ta Kashe kan Ɗan Wasan Najeriya

Osimhen: An Ji Biliyoyin Naira da Man United za Ta Kashe kan Ɗan Wasan Najeriya

  • Napoli da Manchester United na tattaunawa kan siyan Victor Osimhen, yayin da kungiyarsa ke shirin rage farashin dan wasan don saukaka cinikin
  • Cinikiyyar Napoli da United ta kara karfi yayin da Napoli ta ki yarda ta sayar da Osimhen ga Juventus saboda gudun karfafa abokan hamayya
  • Manchester United ta dauki Osimhen a matsayin babban burinta, duk da rashin tabbas na shiga gasar Turai yayin da Arsenal ke bibiyar cinikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Landan - Napoli da Manchester United na shirin kulla yarjejeniya kan siyan Victor Osimhen, dan wasan Najeriya, a kakar cinikin 'yan wasa mai zuwa.

Rahoton ya nuna cewa kungiyar Napoli na shirin saukaka kudin sayar da Osimhen domin ba Manchester United damar kammala cinikayyar.

Magana ta yi karfi tsakanin Man United da Napoli kan sayar da Victor Osimhen
Manchester United na tattaunawa da Napoli domin sayen Victor Osimhen. Hoto: @victorosimhen9
Asali: Getty Images

Giovanni Manna, daraktan Napoli, ya isa birnin Landan domin tattaunawa da jami’an Manchester United kan cinikin dan wasan gaba na Super Eagles, inji rahoton MSN.

Kara karanta wannan

'Dan sandan Najeriya ya rasu a gidan kallon ƙwallo ana wasan Arsenal da Real Madrid

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sha tababa kan sayar da Victor Osimhen

Rahoton ya ce Napoli ba za ta sayar da Osimhen ga kungiyar Juventus ba duk da ta nuna sha'awar hakan, saboda gudun karfafa abokan hamayyar ta na gasar Serie A.

Victor Osimhen wanda ke taka leda yanzu haka a kungiyar Galatasaray a matsayin dan wasan aro, zai bar kungiyar Napoli gaba ɗaya a cikin wannan shekarar.

A bara, Osimhen ya kasa zuwa kungiyar Chelsea da ta Saudiyya, saboda farashin da Napoli ta sanya, amma ana sa ran zai canza sheka zuwa gasar Premier League a bana.

Duk da cewa kudin sayar da Osimhen ya ragu zuwa Yuro miliyan 75, ana ganin Napoli na iya kara rage farashin don kada ya koma Juventus ko wata ƙungiyar Serie A.

Manchester United ta ci burin sayen Osimhen

Jaridar Punch ta ce Osimhen ba zai yi ki ya koma taka leda a Juventus ba, amma akwai sabani tsakanin Napoli da daraktan wasanni na Juventus.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban malami a Kaduna, 'yan sanda, sojoji sun fita nema

Manchester United na bukatar ƙarfafa bangaren gabanta bayan da ta ci kwallaye 37 cikin wasa 31 a gasar Premier League ta bana.

Rudy Galetti ya ce Manchester United ta dauki Osimhen a matsayin babban burinta a cinikayyar 'yan wasa ta wannan bazarar.

Kodayake kungiyar ba ta da tabbacin shiga gasar cin kofin Turai, amma an ce Osimhen yana da sha’awar komawa Old Trafford domin ci gaba da nuna bajintarsa.

Kungiyoyi na sa ido kan cinikiyyar Osimhen

Manchester United ta shirya sayen dan wasan Najeriya, Victor Osimhen
Kungiyoyin kwallon kafa irinsu Arsenal na bibiyar cinikin Victor Osimhen. Hoto: Jose Breton
Asali: Getty Images

An rahoto cewa Chelsea ma ta gana da Giovanni Manna a Landan, amma sun fi mayar da hankali wajen daukar Liam Delap daga kungiyar Ipswich Town.

Enzo Maresca, kocin Chelsea, na ganin Delap zai fi dacewa da tsarin wasan su fiye da Victor Osimhen a wannan kakar.

Rahotanni sun ce Arsenal ta gabatar da tayin siyan Osimhen, yayin da Liverpool, PSG da Barcelona ke sa ido kan lamarin, don ganin ko za su iya shiga cinikin.

Kara karanta wannan

2027: Makomar siyasar Saraki a Najeriya da jita jitar komawa jam'iyyar APC ko SDP

Dangantakar Napoli da United ta kara karfi bayan cinikayyar Scott McTominay a bara, lamarin da zai iya saukaka shirin cinikayyar Victor Osimhen.

Juventus ta mika tayin €75m kan Osimhen

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Juventus ta shirya gabatar da tayin €75m don dauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Dusan Vlahovic.

Za a iya kammala cinikin ne idan Juventus ta samu gurbi a gasar Zakarun Turai ta badi kuma ta kammala sayar da Dusan Vlahovic.

Sai dai kuma, rahoto ya nuna cewa kungiyar Napoli ba ta da niyyar sayar da Osimhen ga Juventus saboda gudun kara karfi ga abokiyar hamayyarta a Serie A.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.