'Dan Sandan Najeriya Ya Rasu a Gidan Kallon Kwallo ana Wasan Arsenal da Real Madrid
- Wani sufeto na ƴan sanda ya faɗi matacce ana tsaka da wasan Arsenal da Real Madrid a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba
- Abokinsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tare suke kallo kwallon kuma ɗan sanda ya yi murnar kowace kwallo da Arsenal ta jefa a ragar Madrid
- Ya ce sai da aka tashi wasan sannan suka fahimci ba ya motsi a kujerar da yake zaune, suka garzaya da shi asibiti amma aka tabbatar da ya mutu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Calabar, Cross River - Wani Sufetan 'Yan Sanda mai suna Stephen Enang ya fadi ya mutu a gidan kallon wasan da Arsenal ta doke Real Madrid da ci 3-0 a daren ranar Talata.
Jami'in ɗan sandan wanda ya kai matsayin sufeta ya rasa ransa ne bayan kammala kallon wasan Arsenal da Real Madrid a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.

Asali: Twitter
Jaridar The Natiton ta tattaro cewa marigayi Enang, dan asalin garin Ekori ne da ke karamar hukumar Yakurr a Jihar Kuros Riba a Kudancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa yana aiki ne a ofishin 'yan sanda na Akim da ke kan titin IBB a birnin Kalaba.
Mutanen da suka san ɗan sandan sun bayyana shi a matsayin mutum mai nutsuwa kuma ɗan a mutun masoyin kungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke ƙasar Ingila.
Ta ya ɗan sanda ya mutu a gidan kallo?
Wani abokin ɗan sandan, wanda ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa Enang yana cikin farin ciki a lokacin kallon wasan a wani gidan kallo da ke titin Abang-Asang.
“Yana cikin walwala sosai kuma lafiyarsa ƙalau, ya yi murna da shewa ta ƴan kallo a kowanne kwallo da Arsenal zura a ragar Madrid."
“Amma bayan tashi daga wasan, lokacin da kowa ke tafiya, muka lura cewa Stephen bai tashi daga kujerarsa ba kamar yadda sauran suka yi. A nan ne muka gane akwai matsala.”

Asali: Getty Images
Yadda aka yi kokarin ceto ɗan sandan
Mutumin ya bayyana cewa an yi ƙoƙarin kai shi asibiti domin ceto rayuwarsa amma rai ya yi halinsa, kamar yadda PM News ta kawom
"A kujerar ya faɗi, muna ta magana amma ba ya ko motsi balle ya amsa, nan dai aka garzaya da shi zuwa Asibitin 'Yan Sanda da ke Akim.
"Duk kokarin da aka yi domin ceto rayuwarsa ya ci tura, daga baya aka tabbatar da cewa ya mutu.
“Shi mutum ne mai halin kirki, mai son kwallon kafa, kuma masoyin Arsenal ne na gaske. Wannan labari ya girgiza mu matuka,” in ji abokinsa.
Duk kokarin da aka yi na tuntubar Jami’ar Hulda da Jama’a na Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Kuros Riba, SP Irene Ugbo, bai yi nasara ba, domin ba ta amsa kiran waya ko sakonnin da aka aika mata ba.
An kashe mai goyon bayan Manchester United
A wani labarin, kun ji cewa wani matashi ya kashe abokinsa kan wasan kwallon da aka fafata tsakanin Liverpool da Manchester United.
An tattaro cewa matashin wanda ke son Arsenal ya hallaka ɗan Manchester United saboda ya yi murnar kwallom da Mohammed Salah ya jefa a raga.
Wannan lamarin ya faru ne Kyobugombe da ke Yammacin ƙasar Uganda bayan wata zazzafar muhawara da ta haɗa su.
Asali: Legit.ng