'Dan Kwallon Najeriya da Ya Zamo Zakaran Afrika Ya Fadi yadda Aka Yi Masa Dariya a baya

'Dan Kwallon Najeriya da Ya Zamo Zakaran Afrika Ya Fadi yadda Aka Yi Masa Dariya a baya

  • Dan wasan Super Eagles, Ademola Lookman ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika na shekarar 2024
  • Lookman ya kayar da manyan yan wasa kamar Achraf Hakimi da Simon Adingra wajen lashe wannan babbar kyauta
  • Dan wasan ya bayyana yadda ya yi fadi tashi a tsawon shekaru da fadan darasi da za a dauka daga kurakuransa na baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Dan wasan Super Eagles, Ademola Lookman ya samu nasara ta tarihi a duniya bayan lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na CAF a shekarar 2024.

An gudanar da taron bayar da kyautar a Marrakech, Morocco, inda Lookman ya zama zakaran Afrika bayan ya kayar da fitattun yan wasa daga kasashe daban-daban.

Kara karanta wannan

'Ka kawo cigaba a Najeriya': Jonathan ya tura sakon yabo da Buhari ya cika 82

Lookman
Lookman ya fadi yadda ya yi fama kafin zama gwarzon dan kwallo. Hoto: @Supereagles
Asali: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa Ademola Lookman ya mika godiya ga Allah kan gagarumar nasarar da ya sammu a rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jawabinsa da ya ja hankula, Lookman ya yi dogon tunani kan gwagwarmayar rayuwarsa, musamman kurakuransa a lokacin wasa a shekarar 2020.

Gwagwarmayar da Ademola Lookman ya yi a baya

Ademola Lookman ya tuna wani babban kuskure da ya yi a shekarar 2020 lokacin yana buga wa Fulham wasa a gasar Premier League.

A lokacin, ya yi yunkurin jefa bugun fanareti na salon Panenka wanda ya gaza saka kwallo a raga, lamarin da ya jawo suka daga kocinsa, Scott Parker da sauran da jama’a.

Scott Parker ya fadawa Lookman cewa:

“Ba za ka iya samun nasara a bugun fanareti da irin haka ba. Duk da cewa shi matashi ne mai koyo, ya kamata ya dauki darasi.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya dura kan Tinubu, ya ce ba zai yi aiki da tsare tsaren 'T Pain' ba

'Dan wasa Lookman ya yi nasara bayan wahala

Lookman ya bayyana cewa duk da wannan kuskure, ya ci gaba da dagewa har ya kai matsayin gwarzon dan kwallon Afrika.

“Shekaru hudu da suka gabata, na gaza a idon duniya. Amma yanzu, bayan shekaru hudu, na zama gwarzon dan kwallon Afrika.”

- Ademola Lookman

Ya kuma shawarci matasa da kada su bari kurakuransu su dakatar da su daga cimma burinsu, ya bukaci su ci gaba da fafutuka.

Ademola Lookman ya yi godiya ga Allah

A cikin jawabinsa, Lookman ya nuna godiyarsa ga Allah, shugabanni, abokan wasansa, da duk wadanda suka ba shi goyon baya.

Ya ce lashe kyautar abin alfahari ne ga kansa, iyalansa, da kasarsa Najeriya kuma za ta karfafa guiwa ga matasan Afrika masu burin samun nasara a rayuwa.

'Yar Najeriya ta ci gasar damben duniya

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2024

A wani rahoton, kun ji cewa jami'ar 'yan sanda mai suna Juliet Chukwu ta lashe kambun Bantamweight a gasar damben duniya.

Bayan samun nasarar, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya ce za su cigaba da goyon bayan jami'ai a fannonin wasanni daban daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng