Bayan Buga Wasa cikin Farin Ciki a Jiya, dan Wasan Super Eagles Ya Rasa Mahaifinsa
- Fitaccen mai tsaron gidan kungiyar Super Eagles a Najeriya, Stanley Nwabali ya yi babban rashi a rayuwarsa
- Nwabali ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 a kafar sadarwa
- Wannan na zuwa ne bayan buga wasa a kungiyar Super Eagles a daren jiya Alhamis da kasar Jamhuriyyar Benin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - An shiga jimami bayan fitaccen mai tsaron gida a Super Eagles, Stanley Nwabali ya yi babban rashi.
Dan wasan ya rasa mahaifinsa ne a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 kamar yadda ya tabbatar.
Mahaifin dan wasan Super Eagles ya rasu
Nwabali ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ne shafinsa na Instagram a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan dan wasan ya kasance cikin wadanda suka bugawa Super Eagles wasa a daren jiya Alhamis 14 ga watan Nuwambar 2024.
Super Eagles ta kara ne da kasar Jamhuriyyar Benin a kokarin neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON a kasar Morocco.
An tashi a wasan kunnen-doki da ci daya da daya wanda hakan ya ba kungiyar Super Eagles damar hayewa domin fafatawa a gasar a 2025.
Tauaron Super Eagles ya tabbatar da mutuwar
Sai dai fitaccen mai tsaron gidan Super Eagles bai bayyana sanadin mutuwar mahaifin nasa ba a cikin sanarwar.
"Ubangiji ya jikanka baba na, ina maka fatan samun gidan aljanna."
- Stanley Nwabali
Yan Najeriya da dama sun jajantawa dan wasan bayan rashin mahaifinsa a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024.
AJSilverCFC ya yi rubutu a shafinsa na X a yau Juma'a inda ya jajantawa mai tsaron ragar kan rashin da ya yi.
Gwamna Fubara ya ba Nwabali kyautar N20m
A baya, kun ji cewa Tun bayan kammala gasar AFCON a kasar Ivory Coast, ‘yan wasan Super Eagles ke samun kyaututtuka daban-daban.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bai wa golan tawagar Super Eagles, Stanley Nwabali kyautar Naira miliyan 20.
Gwamnan har ila yau, ya bai wa sauran tawagar da suka halarci taron kyautar naira miliyan 30 domin kara musu karfin gwiwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng