Lookman: Jerin Kasashen da Suka So Ɗan Ƙwallon Najeriya Ya Lashe Ballon d’Or

Lookman: Jerin Kasashen da Suka So Ɗan Ƙwallon Najeriya Ya Lashe Ballon d’Or

  • Dan wasan Najeriya, Ademola Lookman, ya samu maki 82 daga kasashe 17 a nahiyoyi uku a neman lashe kyautar Ballon d’Or
  • Tauraron na Atalanta ya samu goyon baya mafi karfi daga kasarsa Najeriya, sai kuma kasar Girka da ta ba shi fifiko a Turai
  • Sai dai an yi mamaki ganin Lookman bai samu ko maki guda baya a kasar Italiya, inda a yanzu yake sharafinsa na taka leda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Italy - Dan wasan Super Eagles, Ademola Lookman ya samu kuri’u daga kasashe 17 inda ya zo na 14 a jerin masu neman lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.

An rahoto cewa ‘yan jarida daga manyan kasashe 100 na FIFA ne ke zaben, inda tauraron dan kwallon na Atalanta ya samu maki mai yawa daga kasarsa ta haihuwa.

Kara karanta wannan

Ana masa dawo dawo karo na 2, Jonathan ya yi magana kan nasarar Trump

Dan wasan Najeriya, Ademola Lookman ya samu kuri'un kasashe 22 a neman lashe Ballon d’Or
Ballon d’Or: Dan nwasan Najeriya, Lookman ya samu maki 82 daga kasashe 22. Hoto: @Alookman_/X
Asali: Getty Images

Tsarin kada kuri’a ya bukaci ‘yan jarida su zabi manyan ‘yan wasan su 10, inda ake tantance kimar dan wasa da maki 15 zuwa daya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin mamaki, Lookman ya kasa samun ko da maki daga Italiya, inda yake taka ledarsa yanzu. Dan jaridan Sky Sports, Paolo Condo, ya yi watsi da Lookman a zabinsa.

Kasashen Afrika da suka zabi Ademola Lookman

Sai dai dan wasan mai shekaru 27 ya zo na biyar a Ivory Coast, yayin da Ghana ta sanya shi a matsayi na takwas, kuma Mali ta ba shi matsayi na tara.

Kasashen Afirka da dama da suka hada da Burkina Faso, Zambia, Senegal, Uganda, da Afirka ta Kudu, duk sun zabi Ademola Lookman matsayin na 10.

Gabon da Equatorial Guinea sun nuna goyon baya mai karfi, inda dukkansu suka sanya shi a matsayi na bakwai.

Kasashen Turai da suka zabi Lookman

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da Tinubu ya isa birnin Riyadh, zai halarci manyan tarurruka 2

A Turai, Girka ta fito a matsayin wadda ta ba Lookman goyon baya sosai, inda ta sanya shi na biyu - mafi girman matsayinsa daga kowace ƙasa ta Turai.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Arewacin Macedonia da Ireland duk sun ba shi matsayi na takwas, yayin da Portugal ta amince da rawar da ya taka da kuri'a ta bakwai.

Dan wasan na Najeriya ya samu kuri'u daga Trinidad and Tobago, wadanda suka sanya shi a matsayi na 10, sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta ba shi na bakwai.

Duba cikakken jerin kasashen a nan kasa:

  1. Nigeria – maki 15
  2. Girka– maki 12
  3. Côte d’Ivoire – maki 7
  4. Kamaru – maki 4
  5. Gabon – maki 4
  6. Hadaddiyar Daular Larabawa – maki 4
  7. Equatorial Guinea – maki 4
  8. Jordan – maki 4
  9. Portugal – maki 4
  10. Afrika ta Kudu – maki 3
  11. Ghana – maki 3
  12. Ireland – maki 3
  13. Arewacin Macedonia – maki 3
  14. Finland – maki 2
  15. Mali – maki 2
  16. Moroko – maki 2
  17. Burkina Faso- maki 1
  18. Uganda- maki 1
  19. Trinidad and Tobago – maki 1
  20. Senegal- maki 1
  21. Ukraine- maki 1
  22. Zambia – maki 1

Kara karanta wannan

Malami ya tono badakalar Naira Biliyan 40 da aka yi a majalisa a kasafin 2024

Lookman ya tsallakar da Atlanta

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'dan wasan gaba na Super Eagles, Ademola Lookman ya zura kwallo a wasan da Atlanta da ta buga a gasar Coppa Italia.

Zura kwallon da Ademola Lookman ya yi a karawar Atlanta da Fiorentina ya taimakawa kungiyar tsallakawa zuwa wasan karshe na gasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.