Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya ci Man City a wasan sa na farko a Everton

Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya ci Man City a wasan sa na farko a Everton

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kwashi kashinta a hannu a ranar ranar Lahadi 15 ga watan Janairun shekara 2017, bayan kungiyar Everton tayi mata kaca kaca a gida.

Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya ci Man City a wasan sa na farko a Everton
Lukaku

Da farin wasan kungiyar Man city ta raina Everton, sakamakon ta fara wasan da zafi zafi, sai dai itama Everton ta nuna mata ita ba kanwar lasa bace.

KU KARANTA:Sevilla ta karya alkarin Real Madrid

Romero Lukaku ne ya fara zura kwallo a ragar Man City a minti na 34, daga nan City tayi tayi ta farke amma abin ya gagari kundila. Can zuwa minti na 47 Kevin Mirallas ya kara zura ma City kwallo, daga bisani sai Tom Davies ya karat a Uku a minti 79.

Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya ci Man City a wasan sa na farko a Everton
Dan wasan Najeriya Ademola Lookman

Sai dai gab da tashi, sai sabon dan wasan da suka siya dan Najeriy Ademola Lookman ya zura kwallon karshe ta hudu.

Masana a harkar kwallo sun bayyana rashin sa’ar da City tayi a matsayin mafi tsanani a tun bayan zuwan Pep Guardiola.

Ga bidiyon cin Lookman a nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel