Matashi Ya Hallaka Dan Manchester United da Salah Ya Zurawa Arsenal Kwallo
- An shiga rudani bayan wani dan kungiyar Arsenal ya yi ajalin magoyin bayan Manchester United a kasar Uganda
- Lamarin ya faru ne a kasar Uganda bayan dan Arsenal ya hallaka magoyin bayan Manchester United, Benjamin Okello
- Wanda ya yi kisan da aka bayyana da Onan ya dauki matakin ne bayan Okello yana murnar cin Man Utd da Salah ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kampala, Uganda - Kasa da mako daya bayan wasa tsakanin Liverpool da Arsenal, wani ya hallaka abokinsa kan kwallon kafa.
Wani magoyin bayan Arsenal ya yi ajalin mai goyon bayan Manchester United bayan yin murnar cin kwallo da Mo Salah ya yi.
Menene musabbabin kisan dan Manchester United?
Vanguard ta ce lamarin ta faru ne Kyobugombe da ke Yammacin Uganda bayan wata zazzafar muhawara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar cewa an kashe matashin mai shekaru 22, Benjamin Okello a ranar Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024.
Hakan ya biyo bayan tashi a wasan kungiyar Arsenal da Liverpool inda aka tashi canjaras a filin wasa na Emirates.
Lokacin da Salah ya goge kwallon Arsenal, Okello ya tashi yana murna har da jifa da gyada ga dan Arsenal saboda jin dadi.
Hakan bai yi wa Onan dadi ba, inda bayan tashi a wasan ya buge Okello da sanda wanda hakan ya yi ajalinsa, Daily Monitor ta ruwaito.
Rundunar yan sanda ta samu rahoto
Kwamandan yan sanda a yankin Kabale, Mr. Joseph Bakaleke ya tabbatar da samun rahoton abin takaicin da ya faru kan wasan kwallon kafa tsakanin matasa.
Bakaleke ya ce an garzaya da matashin da ya samu raunuka zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
An kori kocin Manchester United, Ten Hag
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kori kocinta, Erik Ten Hag.
Ana hasashen cewa an kori kocin ne bisa yadda kungiyar kwallon kafar Manchester United ta gaza tabuka abin kirki a bana.
Ko a wasan karshe da Manchester United ta buga da West Ham a ranar Lahadi da ta wuce, kungiyar ta sha wani kaye mai ban ciwo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng