Wulakanta 'Yan Wasan Super Eagles Ya Jefa Kasar Libiya a Matsala, CAF Ta Yi Hukunci
- Wulakanta 'yan wasan Super Eagles ya jefa kasar Libiya a cikin matsala yayin da CAF ta sanar da hukuncin da ta yanke kan zarge-zargen
- Hukumar CAF ta ce ta kama Libiya da karya dokokin dokokin gasar cin kofin Afrika da kuma na CAF a abinda ta yiwa tawagar Najeriya
- An ba Super Eagles maki uku da kwallaye uku yayin da aka ci tarar Libiya $50,000, hukuncin da kasar Libiya ta gaggauta daukaka kara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) ta ba Super Eagles kwallaye uku da maki uku yayin da ta ci tarar dala 50,000 kan 'yan kasar Libya.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Super Eagles ta fuskanci kalubale da suka je Libiya buga zagaye na biyu na sharar fagen shiga gasar AFCON, da suka hada da kwana a filin jirgi.
Kwamitin ladabtarwa ya fitar da hukuncin da ya yi a ranar Asabar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannu Ousmane Kane, wadda aka wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CAF ta hukunta kasar Libiya
Shugaban kwamitin, Kane ya ce hukumar CAF ta yi zama kuma ta cimma matsaya kamar haka:
“An samu hukumar kwallon kafar Libya ta karya sashe na 31 na dokokin gasar cin kofin Afrika da kuma shashi na 82 da 151 na dokokin CAF.
“Libiya ta yi rashin nasara da ci 3-0 a wasa mai lamba 87 tsakanin Libya da Najeriya na gasar AFCON 2025 (wanda aka shirya yi ranar 15 ga Oktoba a Benghazi).
“An umarci hukumar kwallon kafar Libya da ta biya tarar dalar Amurka 50,000. Za a biya tarar a cikin kwanaki 60 bayan sanarwar yanke shawara na yanzu."
Libiya ta yi watsi da hukuncin CAF
Sai dai a cewar rahoton Daily Trust, Libiya ta ce ba a yi mata adalci a hukuncin da ya sanya ta koma kasa a rukunin D a wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON ba.
Don haka mahukuntan Libya sun tuntubi wani lauya dan kasar Tunisiya Ali Abbas domin kare matsayinsu yayin da suka daukaka kara kan hukuncin CAF.
Sakamakon wannan daukaka kara na iya yin tasiri sosai ga wasannin shiga AFCON 2025, musamman ga Najeriya, wacce ke neman karin maki daya domin shiga gasar a Morocco.
'Sun azabtar da mu a Najeriya' - Libiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kwallon kafa a kasar Libya ta yi bayani kan makalewar yan kwallon Najeriya a filin jirgin saman kasarta.
Hukumar LFF ta ce babu gaskiya cikin zargin cewa ta wahalar da yan kwallon Najeriya ne da gangan inda ta ce itama 'yan wasanta sun sha azaba a Najeriya.
Asali: Legit.ng