Ten Hag: Dalilin da Ya Sa Man United Ta Sha Kashi a Hannun Liverpool 3:0

Ten Hag: Dalilin da Ya Sa Man United Ta Sha Kashi a Hannun Liverpool 3:0

  • Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta lallasa Manchester United da ci 3-0 a wasan da suka buga a ranar Lahadi a filin wasanni na Old Trafford
  • A yayin da Luis Diaz ya yi nasarar zura kwallaye biyu a ragar United, shi ma Mohamed Salah ba a bar shi a baya ba, inda ya zura kwallo daya
  • Sai dai manajan United, Erik Ten Hag ya yi ikirarin cewa "manyan kurakurai biyu" suka jawo masu shan kashi a hannun Liverpool

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Manajan Manchester United, Erik ten Hag ya yi ikirarin cewa "manyan kurakurai biyu" suka jawo masu shan kashi a hannun Liverpool da ci 3-0 a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

"Abin da na ke gargadi": Sheikh Gumi ya magantu da Bello Turji ya kona motar sojoji

Manchester United ta yi rashin nasara sau biyu a wasanni uku da suka buga, sakamakon kwallayen da Luis Diaz ya ci da kuma kwallon Mohammed Salah.

Erik Ten Hag ya kare Man United bayan ta sha kashi a hannun Liverpool
Manajan Manchester United ya fadi abin da jawo suka yi rashin nasara a hannun Liverpool. Hoto: @ManUtd
Asali: Twitter

Tawagar United bisa jagorancin koci Ten Hag yanzu suna a matsayi na 14 da maki uku da bambancin kwallaye -3 a gasar ta EPL, inji rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Liverpool ta lallasa United

Idan muka yi nazarin wasan, za mu ga cewa an kashe kwallon farko da Liverpool ta zura a ragar United, inda daga bisani Luis Diaz ya zura kwallaye biyu.

Mohammed Salah ya zura kwallo ta uku bayan mintuna tara da dawowa zagaye na biyu. Ana ganin United ta ci sa'a ba a sake yi mata 5-0 a wasan ba kamar yadda ta faru da su a 2021.

Kocin Man United bai ji dadin yadda wasan ya tashi ba, domin akwai sababbin 'yan wasa shida da ya sanya a wasan bayan da ya sayo su a lokacin sayen 'yan wasa.

Kara karanta wannan

Attajirin duniya Elon Musk ya shiga matsala, Brazil ta hana amfani da manhajar X

Ten Hag ya kare United

A zantawarsa da manema labarai bayan kammala wasan, shafin EuroSport ya ruwaito kocin United, Erek ten Hag na cewa:

"Abu ne mai saukin fahimta. Har aka je mintuna 30 muna a 0-0, amma daga nan ne muka tafka kura kurai biyu wanda ya ba Liverpool nasara.
"Mun yi kokarin mu zura kwallo daya. Joshua Zirkzee ya buga kwallon da ya kamata ta shiga raga amma muka tafka wani kuskuren. Babu jayayya, na jinjinawa kokarin Liverpool.
"Ni ba kamar Harry Potter ba ne, dole ne kowa ya yarda da hakan. Muna da 'yan wasa uku da wannan ne farkon wasansu a wannan kakar."

United za ta shiga gasar Europa?

A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai shakku kan shigar Manchester United gasar cin kofin Europa a kakar wasa mai zuwa, duk da nasarar da ta yi a gasar cin kofin FA.

Kamfanin da ya mallaki United, INEOS, shi ne mamallakin kungiyar Nice wadda ita ma ta samu gurbin shiga gasar, abin da ya sabawa dokar Europa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.