Osimhen Ya Rasa Gurbinsa a Napoli, an Kwace Lambar Rigarsa, Yana Neman Mafita

Osimhen Ya Rasa Gurbinsa a Napoli, an Kwace Lambar Rigarsa, Yana Neman Mafita

  • Fitaccen dan wasan Najeriya, Victor Osimhen ya samu matsala bayan cire shi da aka yi a jerin yan wasan kungiyar Napoli
  • Osimhen ya rasa damar bayan kokarin komawa Chelsea da Al-Hilal da ke Saudiyya ya ci tura a daren jiya Juma'a
  • Wannan na zuwa ne bayan sabon kocin kungiyar, Antonio Conte ya ce Osimhen ba ya cikin tsarinsa na kakar bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Naples, Italy - Dan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen ya rasa girbinsa na taka leda a kungiyar Napoli.

Osimhen ya samu matsala ne bayan kokarin komawa Chelsea da Al-Hilal ya samu tasgaro.

An cire sunan Osimhen daga cikin tawagar kungiyar Napoli a Italiya
Sabon kocin Napoli ya cire sunan Victor Osimhen daga tawagarsa. Hoto: SSC Napoli.
Asali: Getty Images

Napoli: Osimhen ya rasa gurbinsa a kungiyar

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Aminu Ado ya kaddamar da fara sabunta fadar Nassarawa, an yada hotuna

Fitaccen dan jarida, Fabrizio Romano shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Asabar 31 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Romano ya ce Napoli ta kwace lamba tara da Osimhen ke sakawa tare da ba Romelu Lukaku da ya koma ƙungiyar.

Dan jaridar ya ce tuni aka tura sunayen yan wasan kungiyar domin buga wasan kakar bana amma babu sunan Osimhen a ciki.

Alakar Napoli da Osimhen ta kara lalacewa

Wannan na zuwa ne bayan Osimhen ya taimakawa kungiyar samun nasarar lashe gasar Seri A a karon farko cikin shekaru 40.

A yanzu haka dai alaka ta sake lalacewa tsakanin Napoli da Osimhen bayan rashin nasarar ficewa daga kungiyar.

Osimhen ya rasa damar ficewa daga kungiyar Napoli a daren jiya Juma'a 30 ga watan Agustan 2024 har aka rufe kofar cinikayyar yan kwallo musamman a Nahiyar Turai.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

Legit Hausa ta tattauna da wani matashi

Legit Hausa ya tattauna da wani matashi kuma masoyin kwallon kafa a Najeriya kan matakin kungiyar Napoli.

Abubakar Fasa ya ce tabbas abin takaici ne a matsayinsa na dan Najeriya amma akwai laifin Victor Osimhen a lamarin.

Ya ce bayan samun matsala da hukumomin kungiyar ya kamata ya saukar da kai ya karbi tayin Chelsea domin tsira da mutuncinsa.

Fasa ya ce maganar kwace lambar rigarsa kungiyar daga bisani da ba Lukaku lamba 11 madadin ta Osimhen.

Osimhen ya amince da tayin Chelsea

Kun ji cewa akwai alama tataburzar da ake kan yi kan cinikayyar fitaccen dan wasan ƙwallon gaba na Super Eagles, Victor Osimhen ta kusa zuwa karshe.

An ce Osimhen ya amince da tayin da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi masa na biyansa albashin €350,000 (N617.4m) duk mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.