Fitattun 'Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 6 a Turai da Suka Yi Ritaya a 2024

Fitattun 'Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 6 a Turai da Suka Yi Ritaya a 2024

A kakar wasa ta bana wato shekarar 2024 an samu yan wasan ƙwallon ƙafa da dama da suka yi ritaya daga buga tamola.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Hakan bai rasa nasaba da yawan shekarun da suke da shi wanda ka iya kawo musu cikas a harkokin wasanni.

Yan wasan ƙwallon ƙafa a Turai da suka yi ritaya a 2024
Jerin fitattun yan wasa da suka ajiye buga tamola a 2024. Hoto: Emin Sansar.
Asali: Getty Images

Biyu daga cikin wadanda suka yi ritaya a kwallon sun buga gasar EURO ta 2024 da aka buga a Jamus kamar yadda UEFA.com ta ruwaito.

Legit Hausa ta binciko muku fitattun yan wasan da suka yi ritaya a 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Pepe

Dan wasan baya, Pepe ya kasance dan wasa mafi tsufa da ya buga gasar EURO da aka yi a 2024.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo zai yi ritaya daga buga kwallon kafa? CR7 ya bayyana shirinsa

Dan wasan kasar Portugal ya yi shura wurin dakile yan wasan gaba inda ya buga wasa a Real Madrid da kuma FC Porto.

2. Thiago Alcantara

Thiago Alcantara ya yi ritaya ne bayan shafe shekaru hudu a kungiyar Liverpool da ke Ingila.

Tsohon dan wasan ya buga wasanni a kungiyoyin Bayern Munich da kuma Barcelona kafin yin aiki da kocin kungiyar, Hansi Flick a wasannin share fage.

3. Toni Kroos

Kroos ya yi ritaya bayan buga wasan karshe na gasar Champions League da kungiyar Madrid da kuma gasar EURO a Jamus.

4. Wojciech Szczesny

Tsohon mai tsaron gidan Arsenal da Roma ya yi ritaya a jiya Talata 27 ga watan Agustan 2024, cewar Fabrizio Romano.

Wojciech Szczesny ya yi ritaya bayan Roma ta yanke alaka da shi ba tare da sake ba shi damar sabunta kwantiragi ba.

5. Leonardo Bonucci

Kara karanta wannan

Bruno Labbadia: Abubuwa 5 masu mahimmanci game da sabon kocin Super Eagles

Leonardi Bonucci ya ajiye buga tamola bayan barin kungiyar Fernerbahce bayan buga wasa a Juventus da AC Milan na tsawon shekaru.

6. Joe Hart

Tsohon mai tsaron bayan Ingila ya yi ritaya bayan ya bar kungiyar Celtic, Joe Hart ya shafe shekaru a kungiyar Manchester City kafin ya bar kungiyar.

7. Marouane Fellaini

Fellaini ya ajiye buga tamola bayan barin gasar kasar China, tsohon dan wasan kasar Belgium da Manchester United ya sanu wurin tara tulin gashi a kansa.

Ronaldo ya magantu kan ritaya a kwallo

A wani labarin, kun ji cewa Christiano Ronaldo ya bayyana matsayarsa kan batun ritaya a buga tamola nan kusa.

Fitaccen dan wasan da ke buga wasa a Saudiyya ya ce zai yi wahala ya zama koci a kwallo saboda ba shi da sha'awa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.