Tir: Wasu Abubuwan Kunya 5 da Suka Faru da Najeriya a Gasar Olympics 2024

Tir: Wasu Abubuwan Kunya 5 da Suka Faru da Najeriya a Gasar Olympics 2024

Paris - Abubuwa ba su tafi yadda su ka so ga Najeriya ba a gasar wasannin Olympics wanda yake gudana a kasar Faransa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A rahoton nan, Legit ta tattaro wasu abubuwan kunya da suka faru da tawagar kasar Najeriya a wasannin da ake yi a yanzu.

Olympics
Najeriya ta kunyata a gasar Olympics Paris 2024 Hoto: AFP
Asali: Getty Images

Yadda Najeriya ta kunyata a Olympics

1. Rajistar Favour Ofili a Olympics

Daga farawa aka ji Favour Ofili ta na kukan cewa hukumar Najeriya ba ta yi mata rajista ba duk da ta samu gurbin shiga gasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta rahoto cewa kwamitin gasar Olympics na Najeriya ya wanke kan shi, ya ce ba shi ya hana yi wa Ofili rajista ba.

Kara karanta wannan

Tarihin kirkirar jihohi daga 1967 zuwa 1996 da yadda aka samu Gwamnoni 36 a yau

2. Cynthia Ogunsemilore

Ita kuwa Cynthia Ogunsemilore ba ta iya shiga wasan dambe a Olympics saboda ana zargin ta yi amfani da miyagun kwayoyi.

Hukumar ITA mai yi wa ‘yan wasa gwaji ya ce ‘yar damben ta yi amfani da diuretic furosemide, Vanguard ta kawo rahoton nan.

3. Ina keken Ese Ekpeseraye?

Kwamitin gasar Olympic na NOC da hukumar harkar tseren keke watau CFN sun bar Ese Ekpeseraye babu keke a lokacin da ake tsere.

A lokacin da za a fara gudun keke a gasar na Olympics, Ese Ekpeseraye ba ta da keken da za ta hawo, sai Jamusawa suka ara mata.

4. ‘Yan wasan tseren 400m a Olympics

An yi tunanin Najeriya za ta yi abin yabo a gasar tseren mita 400 bayan kokarin Ifeanyi Emmanuel Ojeli, Dubem Amene da Ezekiel Nathaniel.

Abin takaicin da ya faru shi ne a yayin da ake tseren, wani ‘dan wasan Najeriya ya tsallaka zuwa wani sahu, sai aka fatattaki kasar daga gasar.

Kara karanta wannan

Farfesa ya fallasa dabarar turawa wajen shigowa Najeriya da akidun LGBTQ a boye

5. Rashin kayan wasa a Olympics

Leadership ta kawo labari cewa ana ta samun sabani tsakanin ma’aikatar harkokin wasanni da kwamitin NOC da ke shiryawa Olympics.

Ana rigima ne a kan kayan tseren ‘yan wasan Najeriya da ke Faransa. Gwamnatin tarayya ta yi kokarin nuna babu wani karancin kaya.

An kora 'yar Najeriya daga Olympics

A rahoton nan, an kawo cikakken labarin yadda Najeriya ta samu matsala a gasar Olympics, aka dakatar da Cynthia Ogunsemilore.

An dakatar da 'yar damben bayan gaza tsallake gwajin kwaya, ana zargin ta yi amfani da wani sinadarai domin boye kwayoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng