EURO 2024: Ƴan Asalin Najeriya 7 da Suka Buga Gasar Kasashen Turai
A ranar 14 ga watan Yulin 2024 aka buga wasan karshe na cin kofin EURO a kasar Jamus inda Sifen ta yi nasara kan kasar Ingila.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Spain ta samu nasara kan kasar Burtaniya da ci kwallo 2 da 1 wanda ita ce tafi daukar kofin a tarihi da guda hudu.
Tun farkon fara gasar, Akwai zaratan ƴan kwallon da suka yi fice wadanda asalinsu ƴan Najeriya ne da suke bugawa kasashen Turai, cewar Vanguard.
'Yan asalin Najeriya a gasar EURO 2024
Legit Hausa ta binciko muku jerin ƴan wasan da suka bugawa kasashen Turai a gasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Bakayo Saka - Burtaniya
Asalin Iyayen Saka ƴan Najeriya ne amma ya zabi buga kwallon a Burtaniya tun shekarar 2020.
Saka da ke buga wasa a Arsenal ya bayyana soyayyarsa ga Najeriya inda ya ce yana yawan kallon wasan Super Eagles.
2. Jamal Musiala - Jamus
An haifi Musiala a Jamus amma mahaifinsa dan Najeriya ne inda ya zabi ya buga kwallo a kasar Jamus.
Dan wasan tsakiyan mai shekaru 21 ya ce ya so ya bugawa Najeriya kwallo inda ya ce ya shiga rudani wurin zabar inda ya dace.
3. Eberechi Eze - Burtaniya
Iyayen Eze ƴan asalin Najeriya ne da suka haife shi a birnin Landan da ke kasar Burtaniya.
Eberechi yana buga wasa ne a matsayin ɗan wasan gaba a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace a Burtaniya.
4. Manuel Akanji - Switzerland
An haifi Akanji a kasar Switzerland wanda mahaifinsa dan Najeriya ne yayin da mahaifiyarsa yar asalin ƙasar ce.
Dan wasan na Manchester City na daga cikin tawagar da suka lashe gasar Firimiya karo na hudu a tarihi.
5. Noah Okafor - Switzerland
Labarin tsatson Okafor iri daya ne da na Akanji wanda shi ma mahaifinsa ɗan Najeriya ne yayin da mahaifiyarsa ta fito daga Switzerland.
Okafor na daga cikin 'yan wasa da suka buga gasar EURO ta bana da aka yi a kasar Jamus.
6. Michael Folorunsho - Italy
Iyayen Folorunsho ƴan asalin Najeriya ne wanda aka haife shi a birnin Roma da ke Italiya.
Folorunsho yana buga wasa ne a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Hellas Verona da ke Italiya.
7. Joshua Zirkzee - Netherlands
Mahaifin Zirkzee dan kasar Netherlands ne yayin da mahaifiyarsa ta fito daga Najeriya.
Zirkzee ya taimakawa Bologna hayewa gasar zakarun Turai a karon farko kafin komawa Manchester United makon da ya gabata.
Messi ya yi magana kan ritaya
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa a duniya, Lionel Messi ya bayyana kungiyar da zai ajiye tamola.
Messi ya ce zai yi ritaya ne a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami da ke buga gasar 'Major League Soccer' a kasar Amurka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng