Super Eagles: Ahmed Musa Ya Samu Babbar Sarauta a Ziyarar da Ya Kai Masarautar Nguru

Super Eagles: Ahmed Musa Ya Samu Babbar Sarauta a Ziyarar da Ya Kai Masarautar Nguru

  • Sarkin Nguru, Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari ya yi wa Ahmed Musa naɗin sarautar gargajiya ta Shetiman Kwallon Kafa na Nguru a yau Lahadi
  • Shahararren ɗan wasan ya ziyarci jihar Yobe ne domin ƙaddamar da bude gasar cin kofin The AAJ da aka gudanar a Yobe ta Arewa
  • Keftin din tawagar Super Eagles ya nuna matukar godiya ga masarautar Nguru, matasa da daukacin al'umar shiyyar kan karrama shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Yobe - Shahararren ɗan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya samu sarautar gargajiya ta 'Shetiman Kwallon Kafar Nguru' a yau Lahadi, 9 ga watan Yuni.

Sarkin Nguru, Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari ne ya naɗa keftin din tawagar Super Eagles wannan saurata bayan wata ziyara da ya kai fadarsa da ke Nguru, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

Ahmed Musa ya buga kwallo a Yobe
Yobe: Ahmed Musa ya samu sarautar 'Shetiman Kwallon Kafa na Nguru'. Hoto: @Ahmedmusa718
Asali: Twitter

Ahmed Musa ya wallafa bidoyon yadda aka yi masa nadin rawanin sarautar a fadar sarkin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed Musa ya je Yobe buga kwallo

Tun farko dai, Ahmed Musa ya dura jihar Yobe ne domin bude gasar cin kofin 'The AAJ' wanda aka gudanar a shiyyar Yobe ta Arewa.

Tsohon ɗan takarar sanatan mazabar Yobe ta Arewa, Abubakar Abubakar Jinjiri ne ya gayyaci Ahmed Musa domin bude gasar kwallon kafar.

Shahararren ɗan wasan na Arewacin Najeriya ya nuna jin dadi na yadda jama'a suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin su tarbe shi.

Shetiman Kwallon Kafar Nguru na godiya

Ahmed Musa ya rubuta cewa:

"Ina matukar godiya ga mai martaba Sarkin Nguru bisa ganin cancanta ta da ya yi har ya bani sarautar Shetiman Kwallon Kafa na Nguru.
"Hakika zuciya ta na cike da farin ciki da godiya marar misaltuwa. Ina kuma godiya ga matasa da daukacin al'umar Nguru bisa goyon bayan su."

Kara karanta wannan

Ana Fama da Rigimar Sarauta, Sarki Sanusi II Ya Gana da Wasu Manyan Mutane a Kano

Kalli bidiyon naɗin a nan ƙasa:

Ahmed Musa ya magantu kan faɗuwa AFCON

A baya ne muka ruwaito cewa keftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya magantu bayan Najeriya ta gaza cin kofin Nahiyar Afrika na 2023/2024.

Tsohon ɗan wasan gaba na CSKA Moscow da Al Nassr ta Saudiya ya jinjinawa 'yan wasan Najeriya bisa nuna hadin kai da jajurcewa a tsawon wasannin da suka buga a gasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel