2023/2024: Man City Ta Lashe Gasar Premier, Ta Kafa Tarihi a Duniyar Kwallon Kafa
- Kungiyar kwallon kafa ta Man City ta lashe kofin gasar Premier ta bana bayan ta tashi wasanta da ci 3-1
- Phil Foden ya zura wa Man City kwallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya, wanda ya baCity damar lashe kofin
- A yayin da Arsenal ta zo ta biyu a kakar wasan na bana, Saminu Adamu Namunaye ya shaidawa Legit Hausa cewa tawagar ta yi kokari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Man City ta lashe kofin gasar Premier ta bana da aka buga a shekarar 2023/2024, kuma ta lashe gasar karo na hudu a jere, abin da ba a taba yi ba a tarihin gasar.
Man City ta lashe gasar Premier 2023/24
Phil Foden ya zura wa Man City kwallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya, wanda ya ba tawagar Pep Guardiola damar lashe kofin karo na shida a cikin kaka bakwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu wata kungiya a tarihin gasar Ingila da ta taba lashe kofin Premier sau hudu a jere, amma a wannan karon, City ta rubuta sabon tarihi, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.
Kocin na Catalan ya jagoranci tawagar City zuwa lashe gasar Premier shida a cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Arsenal ta gaza lashe gasar tun 2003/04
A cikin wadannan shekaru, tawagar ta haye maki 90 a shekaru hudu. Man City ta matsa lamba a kakar bana domin hana Arsenal cin kofin a karon farko tun bayan shekarar 2003/04.
Gunners ta yi tashi wasanta da ci 0-0 a Etihad a watan da ya gabata wanda ya ba ta tazarar maki daya da City a sauran wasanni tara da suka rage, rahoton Vanguard.
Amma zakarun gasar, ba su yi kasa a gwiwa ba wajen fafatawa a sauran wasannin, inda suka lashe wasanni tara na karshe na gasar, bayan sun zura kwallaye 33.
"Arsenal ta yi kokari a bana" - Namunaye
Wani mai sharhin wasanni daga jihar Bauchi, Saminu Adamu Namunaye, wanda ya zanta da Legit Hausa jim kadan bayan kammala wasannin, ya ce Arsenal ta yi abin azo a gani.
A cewar Namunaye, shekaru 20 kenan kungiyar Arsenal ba ta nuna hazaka a gasar ba kamar bana, kuma magoya bayan tawagar sun yi fatan daga kofin bayan nasara a kan Mancester United.
Mai sharhi kan wasan ya yi nuni da cewa, rawar da Arsenal ta taka a bana zai zama tamkar allura a yayin da za ta tunkari kakar wasa na gaba.
A bangaren Manchester City kuwa, Namunaye ya ce Pep Guardiola ya nuna fikira da kuma kwarewa a wasannin da tawagarsa ta buga duk da kura-kuran da suka samu a baya.
Ronaldo: Dan wasa mafi samun albashi a 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an ayyana Cristiano Ronaldo a matsayin dan wasa mafi samun albashi a duniya, wanda wannan ne karo na hudu da ya ke zama a kan gaba.
Ronaldo ya zama dan wasan da ya fi karbar albashi a duniya bayan da ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudiya inda ya samu kusan dala miliyan 260 a watanni 12.
Asali: Legit.ng