Italiya: Ɗan Wasan Najeriya Ya Yi Bajinta, Ya Taimakawa Kungiyarsa Tsallakawa Wasan Karshe
- Yan wasan Najeriya na ci gaba da samun nasarori a kasashen Turai bayan Ademola Lookman ya zura ƙwallo mai muhimmanci
- Kwallon da Lookman ya ci ta taimakawa kungiyarsa ta Atlanta samun damar tsallakawa zuwa wasan karshe da Juventus
- Kungiyar Atlanta ta yi nasara ne kan takwararta ta Fiorentina da ci kwallaye 4-1 wanda Lookman ya zura ta uku tare da ba da taimakon kwallo daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Italiya - Dan wasan Super Eagles, Ademola Lookman ya zura kwallo a wasan Atlanta da ta buga a gasar Coppa Italia.
Zura kwallon da Lookman ya yi ya taimakawa kungiyar tsallakawa zuwa wasan karshe na gasar.
Kwallaye nawa Lookman ya ci a Atlanta?
Atlanta ta yi rashin nasara a wasan farko da ci daya, inda a wasa na biyu ta yi nasara da kwallaye 4-1 kan Fiorentina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ne kwallon farko da Lookman ya ci a gasar Coppa Italia a wannan kaka kuma kwallo na 10 a dukkanin wasanni a kasar.
Kwallon Lookman a sauya wasan zuwa 3-1 bayan na'urar VAR ta tabbatar da kwallon da ya ci, kamar yadda Atlanta ta wallafa a shafin X.
Yaushe Atlanta za su buga wasan ƙarshe?
Ɗan wasan gaban Najeriya daga bisani ya sake ba da taimako ga Mario Pasalic wanda ya sake zura kwallon na hudu ga kungiyar.
Atlanta za ta buga wasan karshe a ranar 15 ga watan Mayu da kungiyar kwallon kafa ta Juventus.
Hakan ya biyo bayan bajinta sa ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman ya yi a gasar AFCON da aka kammala a kasar Ivory Coast.
Musa ya magantu kan gaisawa da Abba
A wani labarin, kun ji cewa dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya yi karin haske kan kin gaisawa da Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
Musa ya ce ya yi mamaki yadda ake ta cece-kuce kan abin da ya yi ga gwamnan yayin da kai masa ziyara.
Ya ce ya yi hakan ne domin girmamawa inda ya de duk wanda ya san al'adun Arewa ya san hakan ba matsala ba ne.
Asali: Legit.ng