An Dakatar da Paul Pogba Daga Buga Wasa Na Shekaru Hudu, An Fadi Dalili

An Dakatar da Paul Pogba Daga Buga Wasa Na Shekaru Hudu, An Fadi Dalili

  • Kwararren 'dan wasan kwallon kafa, Paul Pogba ba zai taka leda ba cikin shekaru hudu masu zuwa sakamakon dakatar da shi da aka yi
  • An dakatar da tsohon 'dan wasan na Manchester United na tsawon shekaru hudu bayan wani gwaji da aka yi masa a watan Agustan bara
  • Wannan ya dauka hankali sosai a duniyar wasanni yayin da mutane ke cewa wannan matakin na iya kawo karshen wasansa a Juventus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

'Dan wasan Juventus, Paul Pogba ba zai taka leda ba tsawon shekaru hudu masu zuwa saboda an dakatar da shi.

Pogba, wanda ya taba rike kambun 'dan wasa mafi tsada a duniya, yana bugawa Juventus wasa ne a yanzu, amma ba zai taka leda ba a shekaru hudu masu zuwa sai dai inda wani abu ya sauya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 2 sun saduda yayin da suka mika wuya ga 'yan banga a Arewa, sun fadi dalili

An dakatar da Pogba daga kwallon kafa
An Dakatar da Paul Pogba Daga Buga Wasa Na Shekaru Hudu, An Fadi Dalili Hoto: Getty Images/Gabriele Maltinti.
Asali: Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa Pogba bai tsallake wani gwaji mai muhimmanci da aka yi masa a watan Agustan 2023 ba, lamarin da ya sanya aka dauki matakin a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano sinadarin testosterone mai yawa a gwarzon 'dan wasan mai shekaru 30, bayan wasan farko na Juventus a karawarta da Udinese, rahoton La Repubblica.

Hukuncin da aka yanke wa Pogba ya fito ne daga ofishin mai shigar da kara na hana amfani da sinadarin kara kuzari a Italiya ranar Alhamis.

Pogba ya sha alwashin daukaka kara

Lauyoyin 'dan kwallon sun yi ikirarin cewa Pogba ya yi amfani da maganin ne bisa kuskure.

Pogba ya ce zai daukaka kara kan dakatarwar a kotun sauraron kararrakin wasanni. Ba zai iya komawa filin wasa ba sai an soke haramcin.

Masana harkar kwallon kafa sun ce hakan na iya kawo karshen buga wasansa a harkar kwallon kafa domin zai cika shekaru 31 a watan Maris.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili

Idan har hukuncin ya yi tasiri, zai zama yana da shekaru 35 zuwa lokacin cikar wa'din haramcin.

Saudiyya ta dakatar da Ronaldo

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar kwallon kafa ta Saudiyya ta dakatar da fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo.

Hukumar ta dakatar da dan wasan ne wasa daya saboda wani abu da ya yi da ke nuna rashin da'a a wasan da aka gabatar a karshen mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng