AFCON: Tinubu da Gwamnoni 22 Zasu Tafi Kallon Wasan Ƙarshe da Najeriya Zata Fafata da Ivory Coast
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai je kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON wanda tawagar Super Eagles zata kara da Ivory Coast
- Ƴan wasan Najeriya na shirye-shiryen ɓarje gumi da masu masaukin baƙi ƙasar Ivory Coast a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON
- Wata majiya ta kusa ta bayyana cewa Shugaba Tinubu na shirin zuwa har filin wasan domin kallon wasan ƙarshe ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abidjan, Côte d’Ivoire - Rahotanni sun nuna shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Ivory Coast domin kallon wasan da Super Eagles ta Najeriya za ta kara da Cote d’Ivoire a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).
Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu ne za a buga wasan karshe na AFCON 2023 a filin wasa na Alassane Ouattara da ke birnin Abidjan.
Tinubu zai kalli wasan ƙarshe kai tsaye
Yayin da Najeriya ke neman lashe kofin AFCON karo na hudu a tarihin gasar, abokan karawarta a wasan karshe na fatan lashe kofin nahiyar karo na uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani rahoto da Sport Brief ta buga ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024, wata majiya ta yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu zai tafi Ivory Coast domin kallon wasan ƙarshe.
Majaiyar ta bayyana cewa:
"Shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai zo nan kallon wasan ƙarshe tare da mai ɗakinsa (Oluremi Tinubu), na taƙaice muku zance, ana sa ran gwamnoni 22 za su kalli wasan.
"Don haka ranar gida zai cika maƙil, muƙarraban shugaban ƙasa da ministoci ma za su zo kallon gwabzawa da Ivory Ciast."
Idan baku manta ba, kafin zuwan Najeriya wasan ƙarshe, shugaban ƙasa na kallon karawar Super Eagles a gasar AFCON daga gidansa.
Ɗan kasuwa ya mutu yana kallon wasan Najeriya
A wani rahoton kuma kun ji cewa wani ɗan kasuwa ya rasu a filin wasan da Super Eagles ta ɓarje gumi da tawagar Bafana Bafana ta ƙasar Afrika ta Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa fitaccen ɗan kasuwan ya yanke jiki ya faɗi ne tun a filin wasan Stade de la Paix in Bouaké, Côte d’Ivoire.
Asali: Legit.ng