AFCON: Kada Ka Kuskura Ka Dawo Kasarmu, ’Yan Afirka Ta Kudu Sun Gargadi Dan Najeriya, Sun Yi Bayani

AFCON: Kada Ka Kuskura Ka Dawo Kasarmu, ’Yan Afirka Ta Kudu Sun Gargadi Dan Najeriya, Sun Yi Bayani

  • Yayin da Najeriya ke murnar hayewa zuwa wasan karshe a gasar AFCON, mai tsaron bayansu ya shiga matsala
  • ‘Yan kasar Afirka ta Kudu sun gargadi Golan, Stanley Nwabali kan komawa kasar don ci gaba da buga a wasa
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu masoya kwallon kafa a Najeriya kan wannan barazana da aka yi wa Nwabali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

‘Yan kasar Afirka ta Kudu sun gargadi golan Najeriya, Stanley Nwabali kan komawa kasar don ci gaba da buga wasa.

Nwabali wanda ya yi kaurin suna a gasar AFCON da ake yi ya na buga wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta Chippa United a Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da wasu 'yan Najeriya 4 da suka kwanta dama yayin gasar AFCON

'Yan Afirka ta Kudu sun gargadi dan wasan Najeriya kan komawa kasarsu
Yan Afirka Ta Kudu Sun Gargadi Golan Najeriya kan komawa kasarsu. Hoto: @nwabali32, @worldatlas.
Asali: Instagram

Wace barzana aka yi golan Najeriya?

Wannan barazana na zuwa ne bayan shaharar da mai tsaron gidan ya nuna a wasan Super Eagle da kasar a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hira da Channels TV, tsohon dan wasan Najeriya, Idah Peterside ya ce Golan ya samu barazana daga Afrika ta Kudu bayan wasan a jiya.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Peterside ya ce Nwabali ya samu barazanar ce daga magoyan bayan Afirka ta Kudu bayan Najeriya ta doke su a bugun fenareti.

Martanin kungiyar Chippa United

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Chippa United ta nuna goyon bayanta ga dan wasan tun farkon fara gasar AFCON.

Har ila yau, kungiyar ta goyi bayan dan wasan a karawarsu da Afirka ta Kudu inda suka sha suka daga al’ummar kasar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

AFCON: Tsohon hadimin Buhari ya tuna arangamarsa da wani 'dan Obidient a wasan Najeriya

Ta kuma yi alkawarin goyon bayan dan wasan Najeriya a wasan karshe da za su buga da kasar Ivory Coast a ranar Lahadi.

Mafi yawan wadanda suka yi hira da Legit Hausa sun bayyana cewa a yanzu Nwabali ya fi karfin buga wasa a Chippa United.

Yusuf Aliyu da ke kungiyar Manchester City ya ce ba abin mamaki ba ne don PSG ma ta yi wa Lionel Messi bayan cin kofin duniya.

Isma'il Mohammed Madara ya ce:

"Mun yi alkawarin za mu siye shi a Madrid ana gama gasar AFCON saboda yafi karfin zama a Afirka sai dai Nahiyar Turai."

Abdul Barca ya ce:

"Ina tunanin zai yi wahala ma ya koma can saboda akwai alamun wawarsa za a yi a kungiyoyin kwallon kafa a Turai."

Matashi ya mutu yayin kallon wasan Najeriya

Kun ji cewa wani matashi mai bautar kasa ya rasa ransa yayin kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.

Matashin daga jihar Kaduna wanda aka bayyana da Samuel ya na bautar kasa a Numan da ke jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.